Hukumomin kula da jiragen kasa na jihar Xinjiang ta kasar Sin sun bayyana cewa, a shekarar 2022, tashar jiragen kasa ta Horgos dake kan iyakar kasa ta jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin, ta kula da zirga-zirgar jiragen dakon kaya, sama da duba 7 da suka jigilar kayayyaki tsakanin Sin da Turai.
A cewar kamfanin jiragen kasa na Urunqi, matsakaicin adadin jiragen dakon kaya dake kai da koma tsakanin kasar Sin da kasashen Turai da tashar ke sarrafa a kullum, ya kai sama da 19 a ko wace rana a shekarar 2022, wani lokaci har ya kai 27.
Kamfanin ya danganta karuwar shaharar ayyukan hidima ga babban adadin jigilar kayayyaki, da farashi mai sauki, da fafada hanyar sadarwa mai inganci. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp