Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya na tunanin duba yuwuwar yin ritaya daga harkokin siysa gaba daya bayan an kammala zabukan watan Fabrairu zuwa Maris.
Buhari ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar a jiya talata bayan da ya karbi bakuncin jakada na mussaman Evariste Ndayishimiye daga kasar Burundi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya kuma bayar tabbacin cewa, Nijeriya a bisa dankon zumuncin da ke a tsakanin ta da kasashen Afirka, za ta ci gaba da taimakawa kasar ta Burundi.
Buhari da yake yin tsokaci akan bukatar shugaban kasar Burundi a fannin samar wa da Burundi makamashi, musamman man fetur ya ce, ya san yadda kasa ke fuskanta akan karancin makamashi, inda ya sanar da cewa, zai waiwayi kamfanin mai na (NNPCL) domin ya yi dubi akan bukatar ta shugaban kasar Burundi.
Honorable Audace Niyonzima ya ce, shugaban kasarsa ya toro sakon taya ‘yan Nijeriya da kuma shugaba Buhari, murnar shigo wa sabuwar shekarar 2023.