Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya shelanta cewa har zuwa yanzu gwamnatinsa ta dauki harkar ilimi a matsayin sashi da ke kan gaba, ya bayyana cewar ba su wasa da sashin ilimi ko kadan.
Ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da sabuwar makarantar firamare da karamar sakandare ta Alabura a Anguwar Kumbiya-kumbiya da ke fadar jihar, da aka sanya wa sunan shahararren malamin nan, Malam Alabura S. Kudi, lamarin da ya kawo karshen tarihi mara dadi a Anguwar ta Kumbiya-kumbiya kasancewar ta gunduma daya tilo da ba ta da makarantar gwamnati a fadin jihar baki daya.
Makarantar ta Alabura ta kunshi manyan rukunan gine-gine ne guda biyu da ke tattare da azuzuwa 18 kowanne, jimillar azuzuwa 36 kenan, da ofisoshi biyu da manyan ofisoshin taruwar malamai guda biyu, da dakunan kwamfuta na zamani da ake kira e-Library duk dauke da kujeru da kayan aiki na zamani. Hakan makarantar tana da wuri da kayan wasanni da ruwan sha da kyawawan hanyoyi don karfafa harkokin koyo da koyarwa.
Gwamna Inuwa ya ce tun zuwansa mulkin gwamnatinsa ta samu matsalar dimbin yaran da ba sa zuwa makaranta, da lalatattun azuzuwa da kayan aiki a makarantun firamare da sakandaren jihar, kan wannan dalilin ne gwamnatinsa ba ta yi wata-wata ba wajen ayyana dokar ta-baci a fannin na ilimi, wadda tuni ya yi sanadiyyar sauya sashin baki daya.