A yayin taron wakilan jamiyyar kwaminis ta kasar Sin JKS karo na 20 da ya gabata cikin shekarar da ta shude, shugaban kasar Xi Jinping ya taba alli game da yadda JKS ta shafe gwamman shekaru tun kafuwarta, tana aiki tukuru wajen tabbatar da nasarar bunkasa kasa ta hanyar lumana, da ingiza ci gaban rayuwar daukacin alummun duniya.
Ko shakka babu, ga duk mai bibiyar tarihi, ya kwana da sanin cewa, tashe-tashen hankula da yake-yake, ko zaman doya da man ja, wadanda suka wakana tsakanin kasashe daban daban, ba su taba haifar da da mai ido ba. Don haka ne ma shaidun gani da ido, ke dada tabbatar da muradun kasar Sin na bin hanyoyin zaman lafiya domin samun ci gaba, wanda hakan ya zama babban jigo a manufofin diflomasiyyar kasar.
A mahangar kasar Sin, zaman lafiya da ci gaba, tamkar dan juma ne da dan jummai, wato dai muhimman tagwaye ne da ba za a iya raba su ba, don haka mahukuntan kasar ke kara kaimi ga dukkanin hanyoyin raya dangantaka da sauran sassan duniya cikin lumana. Alal misali, Sin ta gabatarwa duniya da shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya”, da dandalin raya hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na FOCAC, ta kuma fadada jarin waje da take zubawa a kasashen Afirka, domin tallafa musu wajen bunkasa tattalin arzikinsu. Wadannan da ma karin wasu manufofin na samar da gata ga kasashe masu tasowa, sun sa akasarin sassan kasa da kasa na kallon kasar Sin a matsayin babbar kawa, kuma aminiyar huldar kasashe masu tasowa, musamman a fannonin samar da ababen more rayuwa, da cinikayya, da zuba jari da hadin gwiwar raya sassan tattalin arziki.
Bugu da kari, kasar Sin na goyon bayan gudanar da cudanyar dukkanin sassan kasa da kasa, da hada-hadar cinikayya maras shinge, da tsaron kasa da kasa, da ayyukan wanzar da zaman lafiya. Tana kuma kaucewa yin mummunar takara ko neman yin babakere, sabanin yadda wasu manyan kasashe musamman na yammacin duniya ke nacewa hakan.
Ko shakka babu, manufofin kasar Sin na wanzar da ci gaba ta hanyar lumana domin cin gajiyar daukacin bil adama, za su ci gaba da haifar da gajiya da dukkanin sassan kasa da kasa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. (Saminu Hassan)