Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun shiga yankin Ushafa da ke a anguwar Bwari a babban birnin tarayyar Abuja, inda suka kashe wani Magidanci, suka kuma yi awon gaba da ‘ya’yansa biyu.
An ruwaito cewa, lamarin wanda ya afku a yau laraba, ya faru ne da misalin karfe daya na rana, wanda hakan ya jefa al’ummar yankin cikin furgici da rudani.
Wata mazauniya a yankin mai suna Veronica David ta ce, lamarin ya afku ne a bayan wata makarantar firamare da ke yankin na Ushafa.
A cewar Veronica, lokacin da ‘yan bindigar suka shigo yankin, sun shafe sama da mintuna 30 suna harbi a sama ba tare da jami’an tsaro sun kawo doki ba.
Ta kara da cewa, kamar yadda muka samu labari wanda suka kashe mai suna mista Adagoke, sun hallaka shine a yayin kokawar da ya yi da su, ganin cewa, ‘yan bindigar sun yi kokarin sace kowa da ke gidan nasa.
Shi ma wani mazaunin yankin mai suna Abul Abbas ya ce, lokacin da yaji harbe -harben bindigun, ya dauka ‘yan bindigar sun yiwa daukacin yankin kawanya ne.