Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) ta ƙaddamar da fara aikin gina katafariyar cibiyar samar da ingantaccen fasfo na zamani a Jihar Ogun da ke shiyyar kudu-maso-yammacin ƙasar nan.
Shugaban hukumar ta NIS, CGI Isah Jere Idris ya jagorancin ƙaddamarwar yayin da ya kai wata ziyara ta musamman a jihar.
Da yake jawabi yayin ƙaddamarwar, Isah Jere ya ce ƙaddamar da aikin ta zo a kan gaɓa bisa himma da ƙoƙarin da NIS ke ci gaba da yi wajen bunƙasa ayyukanta ga ‘yan ƙasa cikin ƙwarewa.
“Wannan aiki da ake ƙaddamarwa a yau zai bunƙasa ayyukan bayar da fasfo a wannan jiha da ta kasance mashigi. Ina taya ‘yan asalin jihar da sauran ‘Yan Nijeriya murnar wannan ci gaba da aka samu saboda zai kawo musu sauƙi wajen samun biyan buƙata daga ayyukan da Babban Ofishin NIS na Jihar Ogun ke gudanarwa ga ‘yan ƙasa”.
CGI Isah Jere ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar ta Ogun Adedapo Obiodun bisa samar da katafaren filin da za a gina cibiyar da kuma haɗin gwiwa da goyon bayan da NIS take samu tun a shekaru da dama daga Gwamnatin Ogun.
“Tabbas, Babban Ofishin NIS na Jihar Ogun yana cin gajiyar gudunmawa da goyon bayan da yake samu daga jihar kuma muna ƙara tsumayar ƙarin haɗin gwiwa a tsakaninmu.
Shugaban na NIS Isah Jere ya ziyarci fadar gwamnatin jihar da fadar babban basaraken Ogun a yayin ziyarar. Haka nan ya kai ziyarar gani da ido a wani kamfani na cikin gida, PROFORCE, da ke kera motoci masu sulke a Iperu da ke Jihar Ogun.