Hukumar Kula da Ma’aikata ta Kasa (NSIWC), za ta fara aikin duba tsarin mafi karancin albashi na kasa a ranar 23 ga watan Janairu.
Ku tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar mafi karancin albashi wanda ya amince da N30,000 ga ma’aikatan tarayya da na jihohi a shekarar 2019.
Sai dai mai magana da yawun NSIWC, Emmanuel Njoku ya ce sun yanke shawarar sake duba mafi karancin albashi na kasa bayan sun gudanar da tarurruka da bayar horo a shirye-shiryen sa ido kan dokar a fadin kasar nan.