Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon gaisuwar bikin bazara ga daukacin Sinawa, yayin da ya gudanar da wani taro ta kafar bidiyo da daukacin al’umma a fadin kasar, gabanin bikin bazara, ko sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa.
Shugaba Xi ya tattauna ta kafar bidiyo da ma’aikatan wani asibiti da wani gidan kula da tsoffi da ma’aikata a wata rijiyar hakar mai da matafiya da ma’aikatan tashar jiragen kasa masu saurin tafiya, da masu saye da sayarwa a wata kasuwa da ‘yan wata karamar kabila ta wani kauye.
Shugaban ya yi bayani kan yadda kasar ke tunkarar annobar COVID-19, yana mai cewa akwai makoma mai haske a gaba. Ya ce kasar ta yi zabin da ya dace na tunkarar cutar da tsauraran matakai cikin kusan shekaru uku da suka gabata, yana mai cewa, kasar Sin ta jure barkewar cutar sau da dama da kuma bullar nau’ikanta.
A cewarsa, kasar Sin ta yi iya kokarinta na rage samun yawan tsanantar cutar da na mace-mace, ta kare rayuka da lafiyar al’umma, wanda ya ba ta dama na saukaka matakan yaki da cutar daga baya.
Ya ce a yanzu, an mayar da hankali ne kan tunkarar cutar ta hanyar amfani da magunguna maimakon kandagarki, da kuma kare lafiyar al’umma da tsanantar cutar. (Fa’iza)