Darakta a hukumar kula da gyare-gyare da raya kasa ta kasar Sin (NDRC), Yuan Da, ya ce tattalin arzikin kasar Sin ya kasance kan gaba cikin manyan rukunonin tattalin arzikin duniya a shekarun baya-bayan nan, inda ya zama wani bangare mai muhimmanci dake ingiza ci gaba tattalin arzikin duniya.
Yuan Da, wanda shi ne daraktan sashen kula da tattalin arzikin kasa na hukumar NDRC, ya ce daga shekarar 2020 zuwa 2022, tattalin arzikin Sin ya karu da kaso 4.5 kan matsakaicin mataki, adadin da ya dara matakin na duniya dake kan kimanin kaso 2.
Hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin, ta bayyana a jiya Talata cewa, tattalin arzikin kasar ya karu da kaso 3 zuwa wani sabon mataki, inda ya kai yuan triliyan 121, kwatankwacin dala triliyan 18, a shekarar 2022.
Da yake misali da tubalin ci gaban tattalin arzikin kasar da bai sauya ba, da ma karuwar kyawawan manufofi da suka haifar da habakar tattalin arzikin, jami’in ya ce kasar Sin na da tabbaci da yanayi da karfin kara inganta baki dayan tattalin arzikinta a shekarar 2023. (Fa’iza)