A yau ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani mai taken “ci gaban kasar Sin ba tare da gurbata muhalli ba a sabon zamani”.
Manufar takarda ita ce, yin cikakken bayani game da ra’ayoyi, da matakan da kasar Sin ta dauka, da kuma nasarorin da ta samu a fannin bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba a sabon zamani, da kuma bayyana wa duniya irin kwarewar da ta samu a wannan fanni.
Jami’in da abin ya shafa ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da inganta zamanintar da zaman jituwa tsakanin bil-adama da muhalli, da hada kai da sauran kasashen duniya wajen gina duniya mai tsabta da kuma kyau. (Ibrahim Yaya)