Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da cewa mutum hudu ne aka kashe tare da yin garkuwa da wani mutum daya a wani kauyen Gambar Sabon Layi da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar yayin da wasu ‘yan bindiga dadi suka yi dirar mikiya a kauyen.Â
A sanarwar da Kakakin hukumar ‘yansandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Lahadi tare da raba wa ‘yan jarida, ya ce harin ya faru ne a ranar 22 ga watan Janairun 2023, kuma cikin gaggawa da samun labarin harin jami’an ‘yan sanda suka isa wajen domin Kai dauki.
Ya ke cewa, “Rundunarmu ta samu kiran gaggawa a ranar 22 ga Janairu, 2022 da ke cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun mamaye kauyen Gambar Sabon Layi inda suka farmaki mazaunan kauyen da ba su ji ba su gani ba.”
“Nan da nan da samun labarin faruwar harin, jami’anmu a karkashin jagorancin babban jami’i (DPO) na reshen shalkwatar ‘yansanda da ke Tafawa Balewa suka isa wajen tare da kwasan wadanda lamarin ya shafa zuwa asibiti domin nema musu kulawar Likitoci.”
A cewarsa bayan kai su asibitin likita ya tabbatar da cewa mutum hudu sun mutu yayin da wani guda ya jikkata da ke amsar kulawar Likitoci a halin yanzu.
Ya kuma kara da cewa maharan sun kuma yi garkuwa da wani mutum guda zuwa wani wajen da ba a sani ba.
Sai dai ya tabbatar da cewa tunin kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Aminu Alhassan ya Bada umarnin a kaddamar da bincike kan lamarin domin tabbatar da an cafko maharan tare da ceto Wanda suka sace.