A yayin da kasar Sin ta daidaita matakanta na yaki na annobar COVID-19, gami da inganta matakan zirga-zirgar Sinawa da na ‘yan kasashen waje cikin sauki da tsari a farkon watan Janairu, kasuwar tafiye-tafiyen da ta yi kusan durkushewa a cikin shekaru uku da suka gabata, ta farfado cikin hanzari a yayin bikin bazara.
Ofisoshin jakadanci da na yawon bude ido na kasashe da dama, ciki har da kasashen Thailand, da Norway da Indonesia, sun yi maraba da masu yawon bude ido na kasar Sin ta hanyoyi daban-daban, tun bayan da kasar Sin ta daidaita manufofinta na yaki da annobar COVID-19, da na shige da fice.
Tururuwar da masu yawon bude ido na kasar Sin ke yi, yana karfafa gwiwa wajen farfado da tattalin arzikin wasu kasashen da suka dogara da yawon bude ido. Ana sa ran kasar Malaysia za ta karbi Sinawa masu yawon bude ido miliyan 1.5 zuwa miliyan 2 a shekarar 2023, yayin da wasu masana a wannna bangare a kasar Singapore sun yi kiyasin cewa, Sinawa masu yawon bude ido, za su samarwa kasar Singapore karin kudaden shigar da suka wuce dalar biliyan 1.5 a shekara. (Mai fassara: Ibrahim Yaya)