A yau Juma’a Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Jihar Osun da ke zamanta a Osogbo ta kori gwamna Ademola Adeleke a matsayin halastaccen zabbaben gwamnan Jihar.
Kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta janye tare da karbe shaidar cin zaben da ta bai wa Adeleke tare da mikawa tsohon gwamna Adegboyega Oyetola.
Hukuncin da shugaban Alkalan Kotun, Mai Shari’a, Tertse Kume, ya karanto, ya ce, Oyetola ne ya lashe zabe da kuri’u 314,931, yayin da shi kuma Adeleke ya samu kuri’u 219,666.