A daidai lokacin da ake fuskantar babban zaben 2023, mahalarta babban taron kamfanin wallafa jaridun LEADERSHIP sun bayyana wasu abubuwa da za su iya taimakawa wajen samun cikakkiyar nasarar zaben da za a gudanar da kuma wadanda ka iya zama cikas ga zabuka.
Taron karo na 14 wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta, tsohon Firayministan kasar Kenya Raiia Odinga ya kasance babban bako mai jawabi inda ya ce, amfani da fasahar kimiyyar sadarwa wajen tattarawa da aikawa da sakamakon zabe ba zai hana magudin zabe ba, don haka dole ‘yan Nijeriya su yi hattara su kuma su zama a ankare don ana iya amfani da kimiyyar sadarwa wajen tafka magudi a zabukkan da ke tafe.
Raila Odinga wandan shaharraren dan siyasa ne a kasar Kenya ya yi jawabi ne mai taken: “Sahihin Zabe A Yayin Farfado da Tattaln Arzikin Kasa”, a taron wanda ya gudana ne a Babban dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja, ranar Talata.
Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana cewa, za ta yi amfani da na’u’rori kimiyya da fasaha da kuma fasahar sadarwa wajen tattara tare da aikawa da sakamakon zabe da zarar an tattara su, amma Odinga ya bayyana cewa, ganin yadda lamarin ya kasance a zabukkan da aka yi a kasarsu ta Kenya a shekarar 2007 da 2022, duk da muhimmanci kimiyyar sadawar amma kuma manyan ‘yan siyasa za su iya karkatar da lamarin su yi magudin zabe a zabukan da ke tafe.
Ya kuma bayyyana cewa, canza alkaluma tare da magudin zabe zai iya haifar da abubuwa masu dama da suka hada da rashin sahihancin zaben da sanya wa masu kada kuri’a su kaurace wa shiga zabuka a nan gaba, saboda al’umma za su gani cewa, kusan duk irin kuri’ar da suka kada ba zai kai ga yin tasiri ba. Ya kuma ce, tafka magudin zabe na koran masu zuba jari a cikin kasa, a kan haka ya yi kira ga kasashen Afirka da su yi hattara da lamarin watsa sakamakon zabe ta hanyar kimiyyar sadarwa su kuma sake tunani a kai.
Ya ce, “Akwai bukatar sake tunani a kan amfani da kimiyyar sadarwa. Ko dai mu yi amfani da sahihin hanyar kimiyya da fasaha wadanda suka hada da na’u’rorin kada kuri’a wanda aka tabbatar da aikinsu a sassaan duniya irin wanda mai kada kuri’a zai iya samun tabbacin kuri’arsa ta samu shiga inda ake so ko kuma amfani da tsarin da muka saba tun da farko.”
Ya kuma gargadi Nijeriya da sauran kasshe Afrika da cewa, nahiyar na iya kasa cimma kuduri na 2063 in aka kasa tabbatar da sahihin zabe don kuma hakan zai kori masu zuba jari.
Ya kuma ce, “In har Afirka na son cimma kudurin 2063, to dole mu tabbatar da gudanar da sahihin zabe a sassan yanki Afrika. Tun da aka kirkiro da tsarin jam’iyyu masu yawa a shekarar 1990 sahihancin zabukkan mu suka ci gaba da tabarbarewa sannu a hankali.
“A kasashenmu da dama gwamnati mai ci ta mallake hukumar zabe, ko kuma a ga wasu manyan ‘yan siyasa sun saka hukumar zabe a cikin aljihunsu ta yadda zai yi wuya a samu gudanar da sahihin zabe gaba daya. Wannan kuma yana faruwa ne saboda yadda ake gudanar da rajistar masu kada kuri’a da yadda ake zaben shugabannin hukumar zaben wanda haka yake kai ga fadawa matsalolin da muke samun kanmu a ciki na tattalin arziki da a zamantakewa.
“A wanan nahiyar ta mu, ya kamata mu fahinci cewa, ba za a tabbatar da cikakken ci gaba ba sai an tabbatar da samar da sahihin zabe, ya zama an samar da gwamnatin dimokradiyya wadda ta samu karbuwa a wajen al’umma gaba daya ta haka ne masu zuba jari za su shigo don bunkasa tattalin arzikin nahiyar.”
Ya kuma kara da cewa, gabatar da sahihin zabe shi ne alamin da zai tabbarwa da masu zuba jari cewa, al’umma ne suka zabi gwamanatin kuma ta doru ne bisa tafiyar doka da oda.
Alhakin Gudanar Da Sahihin Zabe Ya Rataya Ne A Wuyan INEC Da Kotu –Osinbajo
Amma a nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce, samar da sahihin zabe yana a hannun hukumar zabe ta INEC ne da kuma kotunan kasar nan.
Osinbajo, wanda shi ne shugaban taron ya bayyana cewa a tarihin zabukkan da aka gudanar a sassan kasar nan akwai misalai masu dama na yadda tashe-tashen hankula ya shafi sakamakon zabukkan da aka gudanar.
Ya ce, hakan kuma shi ne yake kai ga lalata kayyakin gwamnati dana masu zaman kansu.
Ya kara eda cewa, “Bayan bata lokaci da kuma sakamakon da ake fuskanta bayan tashe-tashen hankula, yadda kotuna suka bayar da hukunci a kan wadanda aka kama da laifukkan zaben shi ne yake kara tabbatar da kuma nuna yadda al’amarin sahihancin zaben zai tabbata gaba daya.
“A baya na yi magana a kan sahihancin hukumar zabe namma a wannan karon ina son kara dubi ne ga muhimmanci da mutuncin kotuna a kan yadda suka yanke hukunce-hukuncen tashin hankalin da aka fuskanta na zabe a kasar nan. Inda aka yi tunanin masu kula da zabukkan sun yi magudi to lallai akwai tashin hankali da babbar matsala.
“Bai kamata a samar da yanayin da al’umma za su fidda da rai da yanke kauna ga hukumar zaben ba, yakamata manyan ‘yan siyasar kasar nan su dubi rayuwa da tattalin arzikin kasa wajen ganin an samu kwanciyar hankali a yayin gudanar da zabe da kuma bayan da aka sanar da samakaon zabukka wannan shi ne kadai zamu iya ba al’ummar mu dama yankin Afirka gaba daya.
Mataimakin shugaban kasan ya ce manyan matsolin da muke fuskanta a kasar nan sun hada da na abinci tufafi, matsalar tsaro.
Osinbajo ya kuma yi jinjina ga wanda ya kafa kamfanin jaridar LEADERSHIP, Sam Nda Isaiah, a kan yadda ya samar da wannan dandamalin na tattaunawa don samar da mafita ga matsalolin da ake fuskanta a Afika
“Ina yaba wa kamfanin ‘LEADERSHIP Media Group’ da kokarin da suke yi na tabbatar da ci gaba wannan akidar ta Sam, muna addu’ar Allah ya gafarta masa.”
Zaben 2023 Zai Zama Ma Fi Kyau A Tarihin Nijeriya –Lawan
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana cewa, zaben da za a gudanar a 2023 zai kasance mafi kyau a tarin kasar nan gaba daya.
Sanata Lawan ya bayyana haka ne a yayin da tawagar Tarayyar Turai (EU) masu sanya ido a zabukkan da za a gudanar suka ziyarce shi tare kuma da tsohon Firayministan Kenyan, Raila Odinga, a ziyarar da suka kai masa a majalisar tarayya Abuja.
Shugaban majalisar ya bayyana wa bakin nasa cewa, majalisar tarayya ta yi kokarin samar da yanayin da tallafi ga hukumar zabe ta hanyar dokoki don a samu yanayin gudanar da sahihin zabukka a fadin kasar nan, ya kuma kara da cewa “Babban zaben da za a gudanar a shekarar nan zai kasance mafi tsari da kyau, wannan na faruwa ne saboda yadda muka samar da dukkan abin da zai kai ga cimma wannan nasarar.
“Tuni Shugaban kasa ya sanya hannu a kan dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima, mun kuma amince da amfani da kimiyyar sadarwa wajen tattarawa da aika sakamakion zabukka, mun kuma yi imanin hakan zai takaita magudin zabe.
Gudanar Da Sahihin Zabe Babban Kalubale Ne –Misis Nda-Isaiah
A jawabinta na maraba da dimbin al’umar da suka halarci babban taron LEADERSHIP, shugabar Kamfanin, Misis Zainab Nda-Isaiah, ta ce, taron a wannan shekarar ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar babban zabe na kasa.
“Nijeriya wadda ke dauke da kusan kashi 16 na al’ummar Afirika tana kuma da tattalin arziki mafi girma, ta samu nasarar gudanar da mulkin dimokradiyya ba tare da katsewa ba na tsawon shekara 24 ya kuma hada kayar da jam’iyya mai mulki ta hanyar kuri’a abin da ya haiifar mana da yabo a sasan duniyar nan, muna kuma godiya ga Allah a kan wanna nasarar.
“Kalubalen da ake fsukanta a halin yanzu shi ne na zaben watan Fabrairu da kuma na watan Maris na yadda za a tabbatar da gudanar da sahihn zabe wanda zai kara samar da kwarin gwiwa ga al’umma kasar gaba daya.”
Za Mu Tabbatar Babu Wani Dan Kasar Waje Da Ya Shiga Zaben – Shugaban NIS
A nashi bangaren, Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), CGI Idris Isah Jere, ya bayyana cewa karramawar da LEADERSHIP ta yi masa a matsayin gwarzon shugaban hukumar gwamnati ta kara karfafa masa gwiwar kara dukufa ga aiki tukuru domin sauke nauyin da tsarin mulkin kasa ya dora masu, inda ya sha alwashin ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren ciyar da hukumar gaba ta kowace fuska.
Idris Isah Jere wanda mataimakin kwanturola janar, ACG Abdullahi Usman ya wakilta wajen karbar lambar yabon saboda uzurin kaddamar da katafaren ofishin NIS na Jihar Katsina da kuma fara bayar da sabon ingantaccen fasfo a can, ya bayyana cewa, “Wannan lambar yabo ta nuna cewa duk abin da muke yi mutane suna kallo, an ga irin ci gaban da muke kawowa na aiki a NIS. Dama daga cikin kuduririn da shi shugabanmu kwanuturola janar na yanzu ya sanya a gaba, akwai batun inganta yanayin aiki da kyautata jindadin jami’ai da tabbatar da tsaron iyakokin kasa da kuma tabbatar da ingancin ayyukan da NIS take yi wa ‘yan kasa. Akwai tsare-tsare da dama na gyaran fuska da ya bullo da su a harkokin bayar da fasfo ta yadda kowane Dan Nijeriya zai iya nema da kansa a duk inda yake ba tare da wani ya shiga tsakani ba.
Haka nan a wurin tsaron iyaka, yana kara daukar matakai musamman wurin amfani da na’urorin fasaha na zamani domin hana bata-gari shigowa cikin kasa ko aikata laifuka da suke da nasaba da iyakokin kasa.”
Ya kuma jaddada cewa babban abin da NIS ta sanya a gaba a halin yanzu shi ne tabbatar da cewa babu wani dan kasar waje da aka bari ya shiga cikin harkokin zaben Nijeriya.
“Kasancewar a yanzu babban abin da ake fuskanta a kasa shi ne batun zaben 2023, NIS ta yi tsayuwar daka tare da daukan kwararan matakai da za su tabbatar da cewa babu wani bako dan kasar waje da aka bari ya shiga cikin harkokin zaben Nijeriya, walau tsayawa takara ko kada kuri’a. Tuni muka yi wannan shiri sosai, sannan kamar yadda aka saba, a ranar zaben za mu kulle dukkan iyakokin kasarmu saboda a tabbatar babu wani dan waje da ya shigo ya yi mana katsalandan a zaben.”
Za Mu Fatattaki Matsalar Sha Da Safarar Muggan Kwayoyi-Marwa
A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Yaki da Safarar Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Brigediya Janar Buba Marwa (Mai Ritaya), ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan ma’aikatan hukumar a kan karramawar da aka yi masa na Gwarzon shekara na LEADERSHIP.
Ya ce, karramawar za ta zaburar da shi don ya kara kaimi wajen fattakar masu sha da safarar miyagu kwayoyi a Nijeriya.
Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da LEADERSHIP bayan ya karbi lambar karramawar a Abuja
Karramawar LEADERSHIP Za Ta Karfafa Ni Wajen Samun Karuwar Nasara –Oramah
A nasa jawabin, shugaban bankin AFREDIM, Dakta Benedict Oramah, ya bayyana cewa, karramawar LEADERSHIP wani abu ne da zai kara karfafa wadanda aka karrama wajen kara zimma a kan abubuwan da suke yi a dukkan harkokin su na rayuwa.
Oramah, wanda aka karrama da Gwarzon LEADERSHIP na shekarar 2022 ya ce, “Karramawar za ta karfafa ni wajen bunkasa ayyukan da ni keyi na tallafa wa al’umma, zan kara a kan abin da nike yi a baya, ina fatan za a cigaba da wannan karramawar don al’umma masu zuwa a bayan mu su bayar da nasu gudummawar.”
Ya kuma yaba wa wanda ya kirkiro da kamfanin na LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah a kan yadda ya jajirce har aka samu wannan dandamalin da ake samar da mafita ga matsalolin da suka shafi Nijeriya dama Afrika gaba daya.
“Wahnan shi ne dalilin da ya sa wannan taron ya zma wani dandamali na samar da mafita ga matsalolin da ake fuskanta na tattalin arziki da siyasa a ga Nijeriya da Afirika , ina mai alfahari da wanan jaridar ta Leadership a kan wannan nasarar.
“A madadin dukkan wadanda aka karrama muna godiya ga kamfanin LEADERSHIP za kuma mu zama wakilai na wanna gidan jaridar a duk inda muka samu kanmu.”
Zan Bunkasa Hukumar NSCDC, Ta Yi Daidai Da Takwarorin Ta A Fadin Duniya – Audi
Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) na daya daga cikin hukumomin da aka karrama a babban taron LEADERSHIP da aka yi ranar Talata, an karrama tane da gwarzon ma’aikatar gwamnati na shekarar 2022 saboda yadda ya kasance tana kare kaddarorin gwamnati a sassan kasar nan.
A tattaunwarsa da manema labarai bayan kammala taron, shugaban hukumar, ya ce, karramarwa za ta karfafa shi da sauran jami’ansa wajen kara gudanar da ayyukansu yadda yakamata.
Ya kuma yi alkawarin cewa, hukumar za ta tsayu wajen ganin ta dakile saye da sayar kuri’a a zaben da za a gudanar a wannan watan da muke ciki kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira a jawabansa a ‘yan kwanakin nan.
Dakta Audi ya kuma yi alkawarin cewa, za su yi aiki tare da dukkan jami’an tsaro don samun nasara dakile dukkan matsalolin staro da za a ci karo da su a zabukkan da za a gudanar a cikin wannan watan.
Shugaba Buhari Ya Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar Nan – Ministan Abuja
Ministan Abuja, Malam Muhammad Bello, ya ce, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi nasarar sake fasalin tattalin arzikin kasar nan a cikin shekara 7 da ta yi tana jagorantar kasar nan, musamman ganin an samar da ci gaba mai dorewa a bangaren albarkatun man fetur da ayyukan gona.
Ministan ya bayyana haka ne a jawabinsa a yayin taron LEADERSHIP da aka yi a Abuja ranar Talara, ya ce gwamnatin Buhari ta mayar da hankal a bangaren da suka shafi harkar noma, hakar ma’adanai, da sauran bangarorin tattalin arzikin Nijeriya.
Ya kara da cewa wadanan matakai na Shugaba Buhari sun taimaka wajen dora tattalin arzikin Nijeriya a kan turbar bunkasa wanda dorewarsa kuma sai an tabbatar da gudanar da sahihin zabe ta yadda gwamnatin da za ta biyo bayan na Buhari ta dora a kai.
Kamfann LEADERSHIP Na Jagorantar Samar Da Zaman Lafiya Da Tsaro A Nijeriya –PSC
Kwamitin bayar da tallafi ga tafiyar Shugaban Kasa (PSC) ta yaba wa kamfanin LEADERSHIP Group, masu buga jaridar LEADERSHIP, LEADERSHIP Friday, LEADERSHIP Weekend da kuma LEADERSHIP Hausa a kan yadda suke jagorantar tabbatar da zaman lafiya musamman a wannan lokacin da ake fuskantar harkar zabe a Nijeriya.
Wakilin shugaban kungiyar, Mallam Gidado Ibrahim, ya bayyana haka a babban taron LEADERSHIP da aka yi a Abuja.
“Ya kamata ‘yan Nijeriya su yi dukkan abubuwan da suka kamata na kauce wa tashin hankali a yayin da ake fuskantar zabukkan da ke tafe, ta haka zabukkan da suke tafe za su kasance cikin kwanciyar hankali ba tare da wasu masatloli ba.
“In aka kauce wa tashin hankali a yayin zabukka, tattalin arzilkinmu zai bunkasa saboda haka muna matukar bukatar zaman lafiya a yayin gudanar da zabukka da bayan zaben gaba daya, ” in ji Ibrahim.