Jami’in ma’aikatar cinikayyar kasar Sin Li Xingqian, ya ce kasar za ta yi amfani da fifikonta na babbar kasuwa, wajen fadada shigo da hajoji masu inganci daga kasashen waje, domin daidaita tsarin cinikayya da samar da hajoji na kasa da kasa.
Li Xingqian, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, ya ce a shekarar 2022, Sin ta shigo da hajojin da darajarsu ta kai dala tiriliyan 2.71. Yayin da darajar cinikayyar kasar da kasashen waje ta kai dala tiriliyan 6.3. Ya zuwa shekarar bara, Sin ta kasance a sahun gaba a duniya wajen yawan cinikayyar kayayyaki cikin shekaru 6 a jere.
Jami’in ya kara da cewa, la’akari da karuwar hadarin fadawa komadar tattalin arzikin duniya, da tafiyar hawainiya da ci gaban bukatun waje ke fuskanta, za a aiwatar da karin matakai na inganta salon cinikayya, da tabbatar da fannin fitar da hajoji ya taka rawar gani wajen tallafawa tattalin arziki. (Saminu Alhassan)