A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon jaje da alhinin aukuwar girgizar kasa ga shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da na kasar Syria Bashar al-Assad, sakamakon aukuwar ibtila’in girgizar kasar da ta shafi wasu yankunan kasashen 2.
Kaza lika a dai wannan rana, kakakin hukumar bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa ta Sin ko CIDCA a takaice, ya ce Sin na ci gaba da tattaunawa da sassan da batun ya shafa a Türkiyya da Syria, kuma a shirye kasar take ta taimaka da tallafin jin kai, gwargwadon bukatar kasashen. (Saminu Alhassan)