Tun daga jiya Litinin 6 ga wata, kasar Sin ta soma dawo da harkokin yawon bude ido cikin rukunoni daban daban zuwa kasashen ketare. Hukumomin yawon bude ido na kasashe da dama sun bayyana fatansu kan hakan, tare da ganin cewa matakin zai karfafa gwiwar sana’ar yawon bude ido ta kasashensu.
Game da haka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Talata cewa, bayan shekaru uku, an sake farfado da sana’ar yawon shakatawa cikin rukunoni zuwa kasashen ketare, wanda hakan zai farfado da kasuwar yawon bude ido ta dukkanin duniya, tare kuma da ba da himma wajen farfado da tattalin arzikin kasa da kasa bayan yaduwar annobar COVID-19. (Mai fassara: Bilkisu Xin)