A yayin da ake ci gaba da jefa kuri’a a zaben kujerar gwamna da ake gudanar wa yau asabar a jihar Ekiti, wasu daga cikin ‘yan siyasa a jihar na rige-rige wajen sayen kuri’un masu jefa kuria ciki har da wasu jami’an tsaro da aka tura domin su tabbatar da tsaro.
Wasu daga cikin masu sanya ido kan yadda ake gudanar da zaben, sun gane wa idanuwansu yadda ‘yan siyasar ke sayen kuri’un masu jefa kuri’ar ciki har da wasu jami’an INEC da aka tura su gudanar da aiki.
An fara gudanar da zaben a cikin kwanciyar hankali, inda masu jefa kuri’ar suka fito da yawansu.
Ana gama kammla tantance masu jefa kuri’ar ne ‘yan siyasar suka fara sayen kuri’un ta hanyar Ajen masu tsare akwatunan zabe.
Misali, a mazaba mai lamba 002 da ke a makarantar firamare ta St Mary Catholic da ke karamar hukumar Oye anga, ‘yan siyasar sun ta kai-komo wurin sayen kuri’u.
Rahotanni na cewa, jamiyyu uku ne suka fi sayen kuri’un, inda ake sayen kowacce kuri’a daga naira 5,000 zuwa naira 10,000 duk guda.