A wannan makon ci gaba ne na hirar da Wakiliyarmu Bushira Nakura ta yi wata fitacciyar Malamar makaranta mai suna Malama Halima Adam Yahaya wadda aka fi sani da Malama Kara da Kiyashi, ta yi bayanin yadda ta samu kanta a sana’ar koyarwa da kuma wasu abubuwa da suka shafi rayuwarta, ga dai yadda hirar ta kasance.
Wadanne irin nasarorin kika samu game da wannan sana’a taki?
Babbar nasara ta a harkar koyarwa ita ce na baiwa yaro ilmi ya koya ya yi amfani da shi ka gina mutum ya zama mutumin kirki har kuma ya taka wani matsayi a rayuwa ita ce babbar nasarar malami.
Shin kin taba ji a ranki cewar dama baki zabi wannan layin na koyarwa ba ko kuwa?.
Ban taba ji ba. Na farko zakiga akwai wasu tarin albarka da Allah ya yi wa malami in kin dauke ladan da yake samu a duniya sannan kuma baka san yawan sadakatuljariyar ka ba ta bangaren abinda ka koya dinbin yara ba. Sannan sa wuya kaga malamin primary da hawan jini don baya mikar data wuce tsahon hannunsa.
Mene ne burinki na gaba game da wannan sana’a taki?
Bani da wani buri. A harkar koyarwa face ace ina raye naga wani dalibi na a mumbari yana wa’azi, ko ya zama wani mai mulki ko wani cikakken mutum abin sha’awa da koyi.
Kamar wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?
To akwai abubuwa na dadi da akasin haka babban farin cikin ma’aikaci yaga an ciyar dashi gaba wato promotion to duk sanda aka yi min shi ina jin dadi sosai. Sannan akwai yaro da naga yana watangaririya yaki makaranta iyayensa sun ki su kaishi na kira shi na yi masa fada daga karshe yaron ya saka kuka nace kana son ka koma makaranta ya ce eh na mai dashi makaranta kullum naga yaron nan Ina jin farin ciki a raina.
Kamar a baya kin taba yin harkar Film, Wane finanai kika fito a ciki? Shin bayan koyarwa kina yin wata sana’a ne kuma nasan kin yi Film abaya ya abin yake?
Eh ina wasu sana’oin ta kayan yara na kukkullawa kuma gaskiya ne na yi harkar Film.
Taya kike fara harkar Film kuma wane irin kalubale kika taba cin karo dasu?
Meye yaja Hankalin ki kika shiga harkar film Kin samu matsala da iyayen ki ko yan uwanki ko kawayenki in kin samu wace irin matsala kika samu?
Wane irin kallo al-umma suke miki kema ya kike kallon al-umma Me zakice da Harkar Film ya kike kallon Harkar Film da koyarwa Da Film din da dana yanzu wanne yafi ci gaba?
Eh na yi harkar film don nice mace ta farko a harkar film nice mace ta farko da a fara baiwa arewa best actress a 2000, na yi films da dan yawa ba laifi na yi ‘Kara Da kiyashi’ ‘Aljannar mace” ,”Mukaddari, “Gimbiya sailuba, suna da yawa wasu ma na mamta sunansu.
Kalubale a harkar film yana da yawa amma babban kaluben Mata a harkar in an zo fagen aure ace mutum kar ya auri ‘yar film basa zaman aure to ni dai alhamdulillah gashi tun 2002 na yi aure gashi ina gidan mijina kuma ina fatan sai mutuwa ce za ta raba. Ada al’umma suna yi min kallon ‘yar film wacce ba za ta iya zaman aure ba sai gashi Allah ya dafa min na zama abin kwatance. Ni kuma a lokacin ina kallon al’umma sun ki min uzirin ina son zaman aure watakila mijin ne Allah Bai kawo ba.
A harkar film nada gaskiya akwai mutuntawa a tsakaninmu da al’umma tunda magidanta da kansu suke gayyatar mu zuwa gidajensu mu gaisa da iyalansu kuma zakiga da yanayin suturun mu zarce ce bama kananun dinku na kuma da wahala ki ganmu ba a gidajen iyayen mu muke ba, Amma yanzu ci gaba ya zo kala kowa da irin tarbiyarsa da halayyarsa da muamallarsa.
Harkar film ba wani ne ya kawo ni ba wata yayar kawatace ta aikemu office din Ibrahim mandawari sai na gan shi na ce inason shiga harkar ya ce na zo rehearsal shike nan na shiga shiyasa nake bugun kirji na ce inda wanda ya kawoni ya daga hannu amma duk da haka har gobe ina da ubangida da kuma wadanda muke zumunci da wadanda suke tallafa wa rayuwa ta sai dai nace na gode musu Allah ya biyasu da aljannah.
Ta bangaren iyaye kuwa ai basu san sanda na fara ba kinsan in kana gidajen ‘yan uwa da yawa to da haka kake fakewa kana zuwa location don ni a sannan banyi tunanin zai fito ba har a gidanmu su gani ba da ya fito kuma a ka nunawa tsohona sai nashiga wasan boya daga baya kuma har ya hakura.
Kawaye kuma ban sami tsangwama daga garesu ba asali ma suna son su ganni a screen su ce ai Halima Adamu ce primary mu daya ko secondary mu daya rayuwar dai a haka nai ta gungurata har zuwa yanzu
Ai film din da yafi dadin kallo Koda iyalanka zaku hadu ku kalla amma na yanzu akwai bakin al’adu da ba za ka so danka ya gani ba ko ya yi koyi dasu.
Wanne kira za ki yi ga matasa musamman mata wadanda ba sa sana’a ba su da abin yi, har ma da manya na gida, me za ki ce akansu?
Kiran da zan yi ga ‘yan uwana Mata su tashi tsaye wajan neman na kansu su daina dogaro da mazajensu don yanzu suma mazan ta kansu suke yi rayuwa ta yi tsada abubuwa sun canza saboda haka adinga karfafa wa maza gwiwa kowacce ta yi hakuri da yanayin da aka samu kai a ciki.
Matasa kuma su dubi girman Allah su nemi ilmi su zage damtse su yi sana’a don zama ba sana’a shike jawo duk wani aikata laifi
Manyanmu kuma muna barar addua su taimakemu su yawaita mana addua a kan halin da rayuwa take yanzu.
Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati game da masu kokarin yin sana’a?
Kira ga gwamnati su taimaka su dinga bada tallafin da zai yiwu ayi sana a Mai Dan kauri domin in hajiya gwamnati za ta bada jari me dan nauyi zaman banza zai ragu sosai km da wahala matasan su cinye jarin lokaci daya Amma an bada 10k 20k tsakani da Allah me matashi zai siya wallahi a teburin indomi zai cinyeta . Wani Yana son sana’a amma ba cikakken jari gwamnati ki duba Mana matasan mu Dan in an dubi matasa to an dubi Al umma ne.
Me za ki ce da wannan shafi na Adon Gari?
Wannan shafi na adon gari yana kokari sosai wajen zakulo Mata daga ko ina domin su basu gudummuwar sa Allah ya karfafi shafin adon gari yasa nan gaba a kara yawansa, nagode kwarai da gaske.
Me za ki ce da Jaridar Leadership Hausa?
Leadership hausa ba karamin ci gaba ta kawo wa harshen Hausa ba muna adduar Allah ya kara tsareta daga dukkan abin ki tare da maaikatanta, Ya tsareta daga tuntuben alkalami ya kara bunkasata, kuma Ina kira ga mahukuntan wannan kamfani da su daure su samarwa da wannan shafi na adon gari ya samu cikakkiyar jarida mai suna LEADERSHIP ADON GARI yadda zamu sakata mu wala da yawa
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Mutanen da zan gaisar suna da yawa na farko babban jigona mahaifina, sai katangata abin jingino na maigida na sai kuma ubangida abin alfahari Barr Muhuyi MAGAJI Rimin Gado, sai kuma dukkan dalibai na tun daga class 2002 zuwa yanzu, ina miko dinbin gaisuwa ta ga kawayen kuruciya na Majami’uttalmiz Gandun Albasa da abokan cin mushe na daliban G.A.S.S.S. Danzabuwa 95 abokan zuwa daji, sai abokan gwagwarma duk inai musu fatan alkhairi.