Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da mambobin rukuni na 19 na jami’an ba da tallafin jiyya da Sin ta turawa kasar Afrika ta tsakiya suka aike masa, inda ya aike musu tare da sauran takwarorinsu dake aiki a kasashen waje da gaisuwa da kuma fatan alheri.
A cikin wasikar da ya rubuta, Xi Jinping ya ce, wadannan likitoci da masu aikin jiyya sun magance matsalolin zaman rayuwa a wuraren, kuma sun jajirce wajen hidimtawa al’ummar wuraren, baya ga kasancewarsu likitoci da ma’aikatan jiyya, har ila yau suna zaman matsayin manzon musamman dake bayyana dankon zumunci dake tsakanin kasar Sin da kasashen waje.
A wannan shekara da muke ciki, ake cika shekaru 60 da Sin ta fara tura rukunin jami’an ba da tallafin jiyya a karo na farko, inda a daidai wannan lokaci, shugaba Xi ya aike da sakon gaisuwa ga likitoci da ma’aikatan jinya da suke aiki ko suka taba aiki a ketare. (Amina Xu)