Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wata ganawar sirri da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele a fadarsa da ke Abuja.
BBC Hausa ta rawaito cewa, Wannan shi ne karo na uku da gwamnan yake ganawa da shugaban tun bayan matsalar karancin takardar kudin kasar na naira da ta bullo a sakamakon sauyin wasu daga cikin manyan takardun kudin na 200 da 500 da kuma 1,000 da Babban Bankin ya yi.
- Abubuwan 5 Da Zaku So Ku Ji A Ganawar Gwamnan CBN Da Shugaba Buhari A Daura
- CBN Ya Tabbatarwa INEC Samun Wadatattun Takardun Naira Don Gudanar Da Zaben 2023
Bayan wannan ganawar tasu ta uku a Aso Villa, Mista Emefiele, ya ki cewa uffan ga manema labarai lokacin da ya fito.
Bugu da kari babu wata sanarwa daga fadar ko wani jami’i na gwamnati da ya bayyana dalilin ziyarar gwamnan bankin zuwa fadar shugaban kasar.
Sai dai duk da haka ana ganin ba za ta rasa nasaba da halin da kasar ke ciki ba na karancin takardun na naira da abin da wahalhalun da al’ummar kasar suka samu kansu a ciki a dalilin canjin.
Ko a ranar laraba da ta wuce shugaban kasar ya gana da gwamnan bankin bayan Kotun Kolin kasar ta dakatar da wa’adin da bankin ya sanya na daina karbar tsofaffin kudin daga ranar 10 ga watan Fabarairu.
Har sai Kotun ta yanke hukunci ranar Laraba da ke tafe, a kan karar da gwamnonin jihohi uku – na Kaduna da Kwara da kuma Zamfara suka shigar a kan batun canjin kudin.