Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce sake farfado da hada-hadar yawon bude ido da Sin ke yi yanzu, zai ingiza bunkasar tattalin arzikin kasar, da kuma kara zurfafa musayar al’adu tsakanin ta da sauran sassan duniya. Kaza lika matakin zai karfafa kwarin gwiwa, da harsashin farfadowar tattalin arzikin duniya.
Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Larabar nan, ya ce wani rahoto ya tabbatar da cewa, yayin da rukunin farko na Sinawa ‘yan yawon shakatawa ya tashi zuwa kasashen waje, karin wasu kasashe na ci gaba da kimtsawa karbar Sinawa masu yawon shakatawa, ta hanyar inganta kayayyakin saukar baki da na bude ido, ta yadda za su janyo hankalin Sinawa masu zuwa shakatawa.
Wang Wenbin ya kara da cewa, Sinawa masu yawon shakatawa sun shigar da sabon kuzari ga farfadowar fannin yawon bude ido, da tattalin arzikin kasashe masu yawo.
Ya ce kafin bullar annobar COVID-19, kasar Sin ce kan gaba wajen yawan masu fita yawon bude ido kasashen waje, a tsawon shekaru masu yawa a jere, kuma Sinawa masu yawon shakatawa na kan gaba wajen yin sayayya, yayin da suke ziyartar kasashen ketare. A gabar da kuma wannan fanni ke farfadowa a yanzu, ana da imanin cewa, fannonin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, da na musayar al’adu da sauran sassan duniya za su kara zurfafa, wanda hakan zai shigar da kuzari, da karin karfin gwiwa ga farfadowar tattalin arzikin duniya. (Saminu Alhassan)