Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya aikewa takwaransa na Equatorial Guinea Manuela Roka Botey, sakon taya murnar kama aiki a ranar 13 ga watan nan.
Cikin sakon nasa, Li Keqiang ya ce Sin da Equatorial Guinea na morewa kawancen gargajiya, da amincewar juna ta fuskar siyasa, suna kuma morar hadin gwiwarsu a fannoni masu tarin yawa.
Ya ce Sin na dora muhimmancin gaske, kan bunkasa hadin kanta da Equatorial Guinea, kuma a shirya take ta yi aiki da kasar, wajen daga matsayin cikakken hadin gwiwa, da kawancen dake tsakanin sassan biyu zuwa wani sabon matsayi. (Saminu Alhassan)