A yau Alhamis ne hukumar harkokin waje ta majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC, ta fitar da sanarwa kan kudurin da majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas, game da amfani da babban balan balan din kasar Sin maras matuki, wanda ya shiga samaniyar kasar Amurka.
Sanarwar ta bayyana cewa, kudurin da majalisar wakilan Amurka ta zartas a baya bayan nan, ya nuna wa al’ummun kasa da kasa zargin cewa wai “Sin na zamewa duniya kalubale”, duba da yadda Amurka ke siyasantar da batun, domin cimma burinta, don haka majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ke matukar suka da adawa da matakin.
Kaza lika sanarwar ta ce, a ko da yaushe, Sin tana bin dokokin kasa da kasa, kuma ba zai yiwu ta gurgunta ikon mulkin yanki, ko dokar keta samaniyar sauran kasashe ba. Kana ta riga ta yi bayani kan batun ga Amurka, da sauran kasashen duniya a kan lokaci.
Sin ta jaddada cewa, babban bala balan din ya shiga samaniyar Amurka ne sakamakon murdawar iska, kuma hakan bai haifar da wani kalubale ko kadan ga tsaron Amurka ba. Don haka take fatan Amurka za ta kai zuciya nesa, ta daidaita batun ta hanyar da ta dace, sai dai maimakon hakan, Amurka ta dauki matakin da ya sabawa dokokin kasa da kasa. (Mai fassarawa: Jamila)