A wannan makon mun kawo maku hirrar da wakiliyarmu Bishira Nakura ta yi da Binta Haruna Abubakar, wata shaharrariyar ‘yar kasuwa, inda ta yi bayani a kan tarihin rayuwarta da kuma yadda ta samu kanta a harkar kasuwanci ga dai yadda hirar ta kasance.
Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki da kuma sunan da aka fi saninki da shi, tare da dan takaitaccen tarihinki.
Assalamu alaikum rahmatullahi wa barakatuhu, da farko sunana Binta Haruna Abubakar (Ummi) amma abokan kasuwancina sunfi sanina da (Maman Nura) an haife ni a karamar hukumar Fagge shekara 1976 na karatuna na addini dana boko dai gwargwado a nan Fagge.
Me ya ja hankalinki har kika fara sana’ar sayar da magungunan mata?
To abinda yaja hankalina har na fara wannan sana’a shi ne ganin na taimakawa ‘yan uwana mata sannan kuma sana’a ta rufin asiri.
Ya farkon fara sana’arki ta kasance, ta wacce hanya kika bi har kika fara, kuma ya kika ji a lokacin da za ki fara, kasancewar wasu na son yin irin sana’ar amma kuma suna tsoro ko kunya, shin ke ma kin fuskanci kanki a irin wannan matsalar ko kuwa?
Tofah a gaskiya lokacin da na fara wannan sana’a banjin wani kunya ba tunda kusan gadanta nayi wajen kanwar babana saboda ‘yar asalin Nijar ne tun tasowa ta naga tana kawowa dan wani lokacin haka zaki ga matan aure har jiran zuwanta suke ta haka na fuskanci lallai wannan ba sana’a bace kawai harda taimakawa ga ma’aurata wannan ne ya ja ra’ayina.
Daga lokacin da kika fara sana’ar kawo iyanzu za ki kai kamar shekara nawa kina?
Eh to akalla zan kai kamar shekara 18 zuwa 20.
Ke kike hada magungunan da kanki ko kuwa sarowa kike yi, sannan ke ma ki dora naki ribar ki siyar, ya abin yake?
A gaskiya ni nake hada kayana tunda na fadama miki kusan gadan sana’ar na yi.
Ya kike ganin yadda karbuwar sana’ar take kasancewa ga su masu siyan, shin kwalliya na biyan kudin sabulu ko kuwa?.
Alhamdulillah tabbas kwalliya tana kan biyan kudin sabulu har yanzu dan wannan sana’a tayimin sutura dama wasu na jikina.
Ta wacce hanya kike bi wajen ganin kin bunkasa kasuwancinki?
Ta hanyoyin sadarwa wato ‘social media’ kamar whatapps facebook sai kuma tiktok.
Za ki ji likitoci da wasu masana na magana game da ire-iren wadannan magunguna wanda mata ke amfani da su, na cewar hakan na iya kawo wa mace matsala, me za ki ce a kan hakan?
Eh toh akwai wandanda basusan me suke ba kawai sauki suke nema da sun ji ance musu ga wani magani yana aiki Kuma kan kudi kalilan sai kiga har rawar kafa suke yi su saya sun sani mai kyau ne a’a marar kyau ne babu ruwan su.
Nata jin wani labarin kan cewa wasu har kashin bera suke dakawa su siyar mata na siya suna matsawa kinga wannan ai illace cutar wa ce mai girma dan ya ja wa mata matsala da dama amma duk macen da tasan kanta tasan abinda ya kamata ta siya ta kuma san gurin wa za ta siya.
Wanne irin kalubale kika taba fuskanta ga su masu siyen, musamman wajen karbar bashi kuma aki biya, ko kuma a siya a samu matsala, ko makamancin haka, me za ki ce a kan hakan?.
Gaskiya ba a taba siyan kayana an samu matsala ba sai dai ma godiya daga wadanda suka siya sai maganar a dauki kaya a ki biya muna fuskanta musamman ta bangaran masu sari dan akwai wata mata da muka fara kamar gaske tan dauka ta kawomin kudin sai da tafiya ta yi tafiya ta dauki kaya masu yawa na daina samu number dinta.
Wadanne irin nasarorin kika samu game da wannan sana’a taki?
Na samu nasarori masu yawa wasu ma baza su faduba.
A ina kike gudanar da kasuwancinki, akwai wani waje ne da kika ware na musamman ko kuwa a cikin gida kike yi?.
A cikin gida nake gudanar da sana’ata sana’ata.
Mene ne burinki na gaba game da wannan sana’a taki?
Burina nan gaba shine ace na bude wani babban shago na zuba yara.
Kamar wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?
Abin da ba zan taba mantawa ba shi ne wata costumer ta yar gana dana taba aikawa kaya a gaskiya na samu alkhairi sosai daga gurinta dan ta silarta na samu costumers sosai a can.
Bayan saida magunguna da kike yi, shin kina wata sana’ar ne ko iya ita kawai kike?
Eh ina saida atamfofi da turararrukan wuta da humra wani lokacin har lefe ana bani na hada amma nafi karfi a magunguna
Idan kina wata sana’ar ya tsarin kasuwancin yake kasancewa, kuma ya bambancin yake kamar wajen yadda sana’ar take kawo kudi da sauransu?.
Gaskiya magani shine kan gaba sha kundum.
Wanne kira za ki yi ga matasa musamman mata wadanda ba sa sana’a ba su da abin yi, har ma da manya na gida, me za ki ce akansu?
Eh ita sana’a rufin asiri ce dan haka ina jan hankalin yan uwan mata da su riki sana’a hannu bibiyu.
Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati game da masu kokarin yin sana’a?
Kirana ga gwamnati shine ta dinga tallafawa matasa duk da tana kokari wajan hakan.
Me za ki ce da wannan shafi na Adon Gari?
Ina mika godiya ta musamman ga wannan shafi na adon gari.
Wanne sako kake da shi ga Leadership Hausa?
Ubangiji ya daukaka wannan gidan jarida ta LEADERSHIP tare ma’aikatanta baki daya.
Ko ki na da wadanda zaki mika gaisuwa zuwa gare su?
Muna godiya.
Godiya ta musamman ga iyayena tare da kannena Sahura (Mai guza) Ummi (Maman al’ansar jigon mata)
Sannan ina gaida jagoran wannan shiri wato Bishira Nakura Nagode.