Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alh. Atiku Abubakar ya gana da masu ruwa da tsaki a PDP tare da kaddamar da yakin neman zabensa a jihar Ribas.
Wazirin Adamawa, ya kuma yi fatan kammala gangamin yakin neman zaben a jihar ba tare wani ya rasa ransa ko an lalata dukiyar jama’a ba.
Shugabannin PDP a kwanan baya, sun ki aminta da gurin da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike wanda kuma jagora ne acikin kungiyar gwamnonin PDP na G-5 ya bayar don gangamin a jihar wanda amma daga baya ya ce ya amince ayi taron a wurin da yaki amincewa na farko.
A ‘yan kwanan baya dai, Ribas ta zamo fagen tayar da rikice-rikicen zabe, musamman idan aka yi dubi da harin da aka kaiwa wasu manyan PDP a jihar ciki har da tsohon ministan sufuri Abiye Sekibo da kuma sanata Lee Maeba.
Har ila yau, an kai wani harin akan wasu shugabanin jam’iyyar SDP da dan takarar gwamna a jam’iyyar sanata , Magnus Abe da kuma dan takarar gwamna na jamiyyar AP Dumo-Lulu.