Yau 20 ga wata, kasar Sin ta fitar da rahoto mai taken “Mulkin danniya da cin zarafi da kasar Amurka ke yi, da ma illar da take kawawo”, inda aka tono yadda kasar Amurka ta nuna kasaita da fin karfi a fannonin siyasa, tattalin arziki da hada-hadar kudi, kimiyya da fasaha, da kuma al’adu, ta hanyar nuna abubuwan shaida, ta yadda kasa da kasa za su fahimci mummunar illar da kasar Amurka ke kawowa duniya a fannonin zaman lafiya da kwanciyar hankali, da muradun jama’arsu. (Kande Gao)