Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a taron manema labaru da aka saba gudanarwa Litinin din nan cewa, a ranar 17 ga watan Fabrairu ne aka gudanar da shawarwari game da kare hakkin bil Adama karo na 38 na Sin da EU a birnin Brussels na kasar Belgium. A yayin tattaunawar, kasar Sin ta gabatar da ra’ayin kare hakkin dan Adam da ya shafi jama’ar kasar ta Sin. Kasar Sin ta bukaci kungiyar EU da ta kalli ci gaban harkokin kare hakkin dan Adam na kasar Sin da idon basira, tare da daina siyasantar da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam, da aiwatar da ma’aunai biyu.
Da yake karin haske game da halin da ake ciki a Ukraine kuwa, Wang Wenbin ya ce, Amurka ce ke ci gaba da ba da makamai a fagen fama, ba China ba. Kasar Amurka ba ta cancanci da umarni ga Sin ba, kuma ba mu taba yarda Amurka ta tsara yadda dangantakar Sin da Rasha za ta kasance ba. A cikin ‘yan kwanaki masu zuwa ne, za a cika shekara daya da faruwar rikicin Ukraine, kasar Sin za ta fitar da takardar matsaya kan yadda za a warware rikicin Ukraine a siyasance. (Mai fassarawa: Ibrahim)