Shugaban hukumar NIS ta kasa Isah Idris Jere, ya kaddamar da fara yin ingantaccen tsarin fasfo na zamani (e-Passport) tare da kaddamar da ofishin fasfo din a birnin Zaria da ke Jihar Kaduna.
Shugaban ya bayyana cewa, Burin hukumar NIS a halin yanzu shine, ci gaba da inganta aikinta ta kowane fanni, musamman a fannin gudanar da fasfo, kula da iyakoki, da jin dadin ma’aikata.
Ingantaccen fasfo na zamanin da aka kaddamar a birnin, kashi uku ne;
- Mai shafi 32 tsawon shekaru 5
- Mai shafi 64 tsawon shekaru 5
- Mai shafi 64 tsawon shekaru 10 amma na masu manyan shekaru ne kawai
Ingantaccen fasfo na zamani (e-Passport) yana da ingantattun nau’uka na tsaro fiye da fasfon na farko (e-Passport), nau’ukan tsaron da aka sa masa bayan ingantashi, ya mai dashi daya daga cikin fasfo na zamani mafi tsaro a Duniya. Yana da shafuka masu nau’i kamar leda wanda hakan tasa yake da juriya ga ruwa, sannan kuma da zarar an sauya wani abu ajikinsa zai nuna shaida.
Nijeriya ce kasa ta farko a Afirka da ta fara yin kaura zuwa irin wannan fasfo; cibiyoyinmu za su cigaba da gudanar da aikin fasfo na zamani da tsoho irin na da, har zuwa lokacin da cibiyoyin za su samu cikakkun kayan aiki don komawa tsarin ingantacce na zamani baki daya.
A yau, yayin da muke kaddamar da wannan ofishin fasfo, Zariya ta shiga jerin cibiyoyin da suke gudanar da ayyukan fasfo a fadin kasar nan da kuma kasashen waje, wadanda suka hada da FCT-Abuja, Lagos, Fatakwal, Canada, UK da Amurka wadanda suka yi nasarar yin kaura zuwa tsarin fasfo na zamani (e-Passport).
Abun ban sha’awa, Zaria ta bambanta da sauran cibiyoyin ta fuskar cewa, ita ce ofishin fasfo na farko a Nijeriya da ke wajen babban birnin jiha.