Jawabin da shugaban Amurka ke yi na shekara-shekara na shekarar 2023 ya zo da kalubale saboda matsalar da ya dade yana fuskanta musamman a lokacin yin jawabi a bainar jama’a.
Sai dai ba shi kadai ba ne, domin akwai wasu sanannun mutanen da suka dade suna neman yadda za su shawo kan matsalar.
- Ra’ayoyinku Da Fatanku Game Da Zaben Shugaban Kasa
- Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Matsayinta Na Warware Matsalar Ukraine A Siyasance
Jawabin da shugaban Amurka ke yi wa ‘yan kasar a kowace shekara daga zauren majalisar kasar abu ne mai sarkakiya ga dukkan shugaba, domin ana sa ran zai gabatar da jawabi mai ratsa zuciya. Sai dai wannan gagarumin aiki ne ga Joe Biden.
Shugaban ya dade yana fama da matsalar in’ina tun farkon rayuwarsa ta siyasa.
Amma in’in ba mutane kalilan kawai ta shafa ba – an kiyasta akwai kimanin mutum miliyan 80 a fadin duniya – wato mutum daya cikin mutum 100 – da ke fama da in’ina.
Jajircewar da Biden ke yi
Akwai kuma kashi daya cikin 20 na mutanen da tun suna kananan yara suke fama da matsalar ta in’ina.
Wannan na nufin ba abin mamaki ba ne a ci karo da fitattun mutanen da ke yin in’ina. Sai dai abin lura shi ne wadannan mutanen ba su cika son bayyana halin da suke cika ga kowa ba.
A misali, Mista Biden ne shugaban Amurka na farko da aka fito fili aka ce yana da in’ina yayin da yake jagorantar kasar.
Wannan ya biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu shugabannin da ya gada kamar Thomas Jefferson da Abraham Lincoln, wadanda suka rayu cikin karni na 18 da na 19 su ma sun yi fama da matsalar.
Amma shugaban mai-ci bai boye tasa matsalar ba, musamman ma a lokacin da suka yi wata zazzafar muhawara da tsohon shugaba Trump a 2020.
Biden ya ce, “In’ina ita ce matsalar da idan ka yi tunani, ta kasance lalurar da har yanzu jama’a ke yi wa mai ita dariya, su kan tozarta mai yin ta”. Mun Ciro wannan daga BBC
Za mu ci gaba a mako mai zuwa idan Allah ya kaimu