Reshen birnin tarayya (FCT) na kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), ta yi tir da da Allawadai da kamawa da tsare Edita Mista Ediri Oyibo da Paul Utebor dan rahoton kafar yada labarai ta yanar gizo, TheNewsGuru.com.
Jami’an ‘yansandan shiyya ta 7 da ke babban birnin tarayya Abuja ce ta cafke su.
A wata sanarwar manema labarai da shugaban NUJ a FCT, Mista Emmanuel Ogbeche ya fitar, ya misalta kamen da aka yi wa ‘yan jarida abun da ba za a lamunta ba kuma kamene da aka yi ba tare da amfani da hankali ba.
A cewarsa, an aike da wasikar gayyata ga Oyibo da Utebo domin yin hira da mataimakin kwamishinan ‘yansanda (DCP), da ke kula da sashin binciken manyan laifuka (CID), wasikar mai dauke da kwanan wata 18 ga watan Fabrairun 2023 amma daga bisani kawai aka cafkesu bayan zuwansu.
Ya ce, “Yansandan sun yi ikirarin a cikin wasikar cewa suna binciken wani kes ne na hada baki, bata suna, bada bayanai na karya da barazana kan rayuwa ga su ‘yan jaridan kan labarin haihuwar wani yaro.
“Zuwan ‘yan jaridan ke da wuya ne ‘yansandan suka kama ‘yan jarida kan wani takardar korafi da Adaobi Alagwu da cewa sun wallafa wani labari da ke cewa tsohowar shugaban bankin Skye, Tunde Ayeni ta karyata yi zargin cewa ba ita ce ta haifi danta ba.
“Yan jaridan, wadanda suka shafe tsawon kwanaki hudu a tsare cikin yanayi marar kyau, sannan an ki bada belinsu ba duk da ganawa da aka yi ta yi, sannan an nemi su kawo ma’aikacin gwamnati mai matakin aiki da bai yi kasa da level 14 a matsayin mai tsaya musu ba.
“Abun mamaki, bayan cika sharadin belin, a ranar Juma’a ga watan Fabrairun 24, cikin gaggawa ‘yansandan suka je suka gurfanar da su a gaban kotun majistire a cikin FCT da ke Wuse Zone 6 amma sun samu kotun ba zauna ba. Amma ‘yansandan sun cigaba da tsaresu ta haramtaccen hanya.
“NUJ tana bukatar a gaggauta sake Mr. Ediri Oyibo da Paul Utebor sannan muna neman ‘yansada su cigaba da bin hanyoyin da suka dace wajen gudanar da ayyukan da ke gabansu.”