Ameerah Sufyan, wadda aka ce an yi garkuwa da ita, ta nemi afuwar jama’a da hukumar ‘yan sanda tare da neman cewa ayi mata Addu’a
Sufyan, masaniyar ilimin halayyar dan adam, ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin cewa “tunani mara kyau ne ya je fata yin garkuwa da kanta.”
“Barkanku mabiyana, Ina so in nemi afuwarku, da daukacin sashen ‘yan sanda, da abokaina da ‘yan uwana kan cewa anyi garkuwa dani, babu wani abu da ya faru kuma duk wannan rudi ne da tunani mara kyau.
“Ina kuma mika godiyata ga IG da CP Babaji Sunday da suka bazama neman ceto ni, Allah Ya saka musu da alheri.”
Ameerah ta bayyana yadda lamarin ya faru kamar haka:
Da gangan na fita daga gidanmu, na tafi daji, na azabtar da kaina da kishin Ruwa da yunwa na tsawon kwanaki hudu.
Ta tabbatar da cewa “babu wanda yayi garkuwa da ita ko kadan.”
A ranar 14 ga watan Yuni ne Ameerah ta wallafa a shafinta na Twitter cewa wasu mutane sanye da kakin ‘yan sanda da bindigogi a wata mota sun sace ta tare da wasu mutane 16 daga sassa daban-daban na Abuja.