Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta bayyana a yau cewa, bisa gayyatar da ministan harkokin wajen kasar India, kasar da ke shugabantar kungiyar G20, Subrahmanyam Jaishankar ya yi masa, ministan harkokin wajen Sin, Qin Gang, zai halarci taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 a birnin New Delhi na India a ranar 2 ga watan Maris.
Da take bayani game da fatan kasar Sin kan taron, Mao Ning ta ce yanzu haka, duniya na fama da tashin hankali, kana farfadowar tattalin arzikin duniya ba shi da kwari, kana ana fuskantar tarin kalubale wajen aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa zuwa 2030 na MDD. Ta ce a matsayin wani dandali na hadin gwiwar kasa da kasa kan raya tattalin arziki, kamata ya yi kungiyar G20 ta mayar da hankali kan shawo kan kalubalen da ake fuskanta a duniya a fannonin tattalin arziki da neman ci gaba, da kara taka rawa wajen inganta fafadowar tattalin arziki da ci gaban duniya.