Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, Amurka ce ta fi haifar da barazanar nukiliya a duniya.
Kalaman na Mao na zuwa ne a yayin wani taron manema labarai da aka saba shiryawa Jumma’ar nan, lokacin da aka nemi ta yi karin haske kan rahotannin da kafafen yada labarai suka bayar cewa, mai baiwa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaron cikin gida Elizabeth Sherwood-Randall ta bayyana cewa, Amurka na bukatar hadin kan kasar Sin a kokarin rage barazanar nukiliya.
Ta kara da cewa, kasar Sin ta kasance mai yin taka tsan-tsan game da manufofinta na nukiliya, tare da bin dabarun kare kai, da manufar nan ta ba za ta fara yin amfani da makamin nukiliya ba da kiyaye karfinta na nukiliya a matsayin mafi karanci da tsaron kasa ke bukata.
A cewar Mao, ya kamata Amurka, a matsayinta na kasa mafi karfin makaman nukiliya, ta martaba manufar nukiliyar da ta dace. Sai dai kuma, a cikin ‘yan shekarun nan, kasar Amurka ta kashe kudade masu tarin yawa, don inganta karfin nukiliyarta, da habaka matsayin makaman nukiliya a manufofinta na tsaron kasa da kafa kawancen soja a sassan duniya.
Don haka, ta yi kira ga kasar Amurka da ta dauki matakan da suka dace, don rage hadarin nukiliya da kuma yin aiki bisa gaskiya, don kiyaye dabarun zaman lafiya da tsaro na shiyya da ma duniya baki daya. (Ibrahim)