Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta ceci rayukan jama’a da dukiyoyin 46 da kudinsu ya kai Naira miliyan 95.4 daga gobara 82 da aka samu a cikin watan Fabrairu.
Hukumar ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Juma’a a Kano.
- Gobara Ta Kone Hedikwatar ‘Yansanda A Kano
- Ganduje Ya Jajanta Wa Rundunar ‘Yansandan Kano Kan Gobarar Da Ta Tashi A Ofishinta
Abdullahi ya bayyana cewa mutum 8 ne suka rasa rayukansu, yayin da gobara ta lalata dukiyoyin da suka kai na Naira miliyan 31.8.
“Mun amsa kiran ceto 35 da amsa kiran Æ™arya 13 daga mazauna jihar,” in ji shi.
Kakakin ya shawarci mazauna garin da su rika kula da gobara domin gujewa hasara.