Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Cote d’Ivoire ya gudanar da bikin murnar cika shekaru 40 da kulla huldar diplomassiya tsakanin Sin da Cote d’Ivoire a birnin Abidjan, cibiyar tattalin arzikin Cote d’Ivoire a jiya Jumma’a.
Firaministan kasar Patrick Asch, karamin minista kuma ministan kula da harkokin waje da dunkulewar kasashen Afirka da ‘yan asalin kasar dake ketare, Candia Camara, da mukadashin wakilin ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Cote d’Ivoire Zhou Kangning, sun halarci liyafar.
Camara ta bayyana a cikin jawabinta cewa, bangaren Cote d’Ivoire yana tsayawa tsayin daka wajen martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, tana kuma fatan hada kai da bangaren Sin don ci gaba da inganta da habaka hadin gwiwa a fannoni daban daban, da samun bunkasuwa tare, da nufin gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil’adam.
A nasa jawabin Zhou Kangning ya yi nuni da cewa, bangaren Sin yana son hada kai da bangaren Cote d’Ivoire, bisa jagorancin ra’ayi daya da aka cimma a yayin tattaunawar shugabannin kasashen biyu, da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Cote d’lvoire, zuwa wani sabon matsayi, ba da babbar gudummawa ga gina makomar bai daya ta bil’adam mai inganci a cikin sabon zamani. (Safiyah Ma)