Ci gaba daga shafi na makon da ya gabata
Asalin Tattar
Asalin Tattar (kuma ana ce masu Mugul) kabilu ne na kasar Sin (China). Suna da jinin turkawa, kai a Turkiyyah ma babu kabilar da ta kai yawan ta su a wancan lokaci. Ba a taba samun labarin su ba sai da suka bayyana kwatsam a karshen karni na shida; shekarar 599H karkashin jagorancin sarkinsu Jinkizkhan (Sarkin duniya). Amma an samu labarin cewa kafin haka, sun yi ta fadace- fadace tsakanin junansu, bayan galabar
Jinkizkhan ne suka bullo ma al’ummar Musulmi.
Tattar mutane ne masu bautar rana, kuma sun yi imani cewa, tun da Allan da yake sama guda daya ne to dole ne a duniyar kasa a samu sarki guda, don haka suke yaki a kan tabbatar da wannan manufa. A addininsu babu haramun; komai ana iya yi. Don haka suna cin kare, suna cin alade, kuma ba sa aure; kowa na iya zo ma macce, ba wanda ya san dan wani.
Suna da kishin kasa wanda ya zarce iyaka. A cikin su akwai masu da’awar Musulunci, suna kalmar shahada, suna kuma ganin girman Musulmi amma ba su yakar kowa sai a kan ‘yan kasancin nan nasu.
Shigowar Tattar a Biranen Musulunci:
Wuri na farko da Tattar suka fara kai hari shi ne Bukhara, inda suka yi angaya a bayan wannan babban birni. Suka kwana uku suna gwabzawa da mayakan Musulmi. Daga karshe dai da yawan sojojin Musulmi suka gudu saboda bala’in da suka gani wanda basu iyawa da shi.
Suka tasar ma Khurasana. Mutanen gari ba su samu wata mafita ba sai dai su yi saranda su nemi a ba su lamuni a kan rayukansu. Alkali Badruddini ne ya jagoranci masu neman wannan sulhun.
A ranar 4 ga watan Zhul Hajji 616H aka buda ma Tattar kofofin gari, suka shiga da makirci suna masu nuna tausayawa da kyautatawa ga mutane. Jinkizkhan ya nemi mutanen Bukhara su kama masu don su yaki sojoji 4000 da suka shiga Kal’ah wadanda ba su samu tserewa ba, ya ce kuma duk wanda bai je ba za a kashe shi.
Ya kuma ba da umurni a cike babban ramin da sojojin suka yi garkuwa da shi har ya sa aka rika dauko Alkur’anai daga masallaci ana zubawa cikin ramin don a cike shi.
Aka kuma dauko mimbarin masallaci aka kakkarya katakonsa don a zuba cikin ramin a cike shi.
Da haka suka isa wannan wuri suka gama da duk sauran sojojin da suka rage ma Musulmi. Bayan haka ne sarkin Tattar ya ce a rubuta masa sunayen muhimman mutanen gari, ya sa aka rinka kiran su guda-guda, aka kwace duk wani makami ko wata dukiya da ke hannunsu, sannan aka yi musu yankan rago baki daya.
Sannan aka kewaye sauran Musulmi aka rinka kisan su, aka farauci matansu da ‘ya’yansu aka rinka aikata alfasha da su gaban mazajensu.
Wadanda suka samu iya tserewa suka gudu, wasu kuma suka auka cikin makiya da makamai suka samu shahada, cikinsu har da babban malamin fikihun nan Ruknuddin Zadah da alkali Sadruddin Khan. Wasu kuma aka kama su ga hannu. Kai, a takaice dai Tattar ba su bar birnin Bukhara ba sai da suka kunna masa wuta, suka kone masallatai da makarantu da gidaje babu iyaka, suka azabta fursunonin da suka kama matsananciyar azaba.
Inna lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.
Daga nan suka tasar ma Samarkanda, suka gargado fursunonin Musulmi kamar a waki a gabansu, wanda duk ya kasa tafiya sai su kashe shi su wuce. Suka mika wa ko wane Musulmi tuta ya daga don a tsorata jama’ar Musulmin Samarkanda. Da isowar su ba su bata lokaci ba suka gwabza da rundunar Musulmi suka kashe soja 50,000 sannan suka far ma farar hula.
Daga baya sai suka rinka ja da baya suka zame jiki Musulmi na bin su, ashe wata makida ce suka shirya sai da aka fita garin gaba daya sai suka yanke wata gada da suka haka suka yi wa Musulmi kimanin 70,000 zobe suka kuma yi musu kisan kiyashi.
Su ma dai sauran mutanen da aka baro a cikin birni sai da wancan bala’in da ya cimma mutanen Bukhara ya cimma su. Suka nemi sulhu, Tattar suka ba su, kuma suka yaudare su.
Aka nemi su bude kofofin gari, sannan su fito da dukiyoyin da duk suka mallaka, sannan su yo waje da dabbobinsu da matansu da ‘ya’yansu.
Aka ce masu za mu kai ku wani wuri inda za ku rayu, daga karshe aka kora su zuwa titin alkiyama baki daya. Sannan aka kona babban masallacin gari, aka ci mutuncin budare Musulmi da rana tsaka, aka aikata fasadi wanda ba zai fadu ba. Duka wannan ya faru a cikin watan Muharram na shekarar 617H.
Birane biyu da muka fada a baya, Bukhara da Samarkanda mun fade su ne kawai a matsayin misali. Amma bala’in ‘yan Tattar bai tsaya a kansu ba domin sai da suka tsallaka tekun da ake tsammanin ba wata runduna da za ta iya tsallaka shi.
Ba su da jirgin ruwa ko guda, amma dawakansu sun iya ruwa, don haka sai suka shirya wasu manyan akwatuna suka zuba makamansu a ciki sannan suka sa masu fatun shanu don kada ruwa ya lalata makaman, sannan kowanensu ya rike wutsiyar dokinsa, ya daura akwati a kugunsa. da haka suka tsallaka ruwa. Kwatsam! Sai aka ji su a garin sarki Khuwarizm Shah. Suka tarwatsa Naisabur da Mazandaran da Rayy (Tehran) da Hamazan da Azrabejan da Irbil da duk sauran garuruwan Musulmi da ke tsallaken tekun Jehon. Duk kuma inda suka je su kan yi amfani da fursunoni Musulmi da suka kamo a gari na baya su yi garkuwa da su, sannan in sun gama su kashe su. Wani lokaci kuma idan Musulmi suka buya bayan yaki ya yi zafi sai Tattar su sa fursunonin da ke tare da su su yi kira cewa jama’a ku dawo! makiya Allah sun tafi. Sai sun fito sai su gamu da gamon su. Su kuma in sun ki a kashe su.
Wani abin ban tsoro a game da sha’aninsu shi ne cewa, bayan karfi da suke da shi mutane ne masu nacin gaske. Misali sa’adda sojojinsu suka zo birnin Khuwarizm wata 5 suka yi a kewaye da shi kafin su samu buda shi. A birnin Talikan sun gamu da mayakan da suka buwaye su, amma sai suka kewaye shi har tsawon wata 6, duk ba su ci nasarar karya shi ba.
Sai da Jinkizkhan ya zo da kansa sannan ya sake yi wa garin zobe na tsawon wata hudu sannan ya iya karya shi, ya kashe duk al’ummar da ke cikinsa. A takaice dai babu shakka Musulmi sun wulakanta matuka a wancan lokaci, kuma tsoro ya shige su da tashin hankali wanda babu irin sa. Har ta kai mayaki daya daga cikin Tattar zai iske mutane dari suna fira ya hau su da sara da kisa har ya kai karshen su gaba daya ba a samu wanda ya kashe shi ba.
Wani ma sai ya kwantar da Musulmi sannan ya ce, na manta takobina ka tsaya nan har in dawo, kuma Musulmin ba zai daga ba saboda tsananin razana da mika wuya. Wata mata daga cikinsu ta shiga wani gida ta karkashe mazaje da dama ta kama wasu sai daga baya suka gane macce ce sannan wani daga cikin su ya samu sa’ar kashe ta.
Labaran kamar yadda muka fadi a baya in mutum na jin su kamar ba zai gaskata ba.
Babbar Musiba:
Faduwar Bagadaza. Duk abin da Tattar suka yi a baya bai taka kara ya karya ba in aka ambaci labarin abin da suka yi ma shedikwatar Musulunci ta Bagadaza. Ita dai Bagadaza Allah ya sa mata kwarjini a idon Tattar kasancewar ta shedikwatar daular Musulunci ta duniya gaba daya. Amma hukuncin Allah ya kaddari cewa, sarki mai ci a wancan lokaci Halifa Musta’asim billah ya yi sakarcin da ya mika wani babban mukami ga wani dan Shi’ah shi ne Ibnul Alkami wanda shi ne ya hada kai tare da Khawwaja Nasiruddin Al-Dusi – suka jawo Tattar suka kwadaitar da su ga kama wannan birni.
Siyasar da Waziri Ibnul Alkami ya bi ita ce, ya yi duk kisisinar da ya sa aka mayar da sojoji a karkashin ofis dinsa, sai ya yi ta korar su aiki, tun suna 100,000 har suka dawo kimanin 10,000. Ya bar sauran babu albashi na tsawon lokaci, ya kwace musu makamai, ya lalata aikinsu. Har ta kai ma sojoji sun koma ‘yan maula don neman abinci, ba su da kwarjini ko kadan har zanbo mawaka ke yi musu.
Sannan sai ya rubuta ma sarkin Tattar yana kwadaitar da shi ga daular Ahlus-Sunnah yana yi masa alkawarin ba shi cikakken hadin kai.
Haka kuwa aka yi. Da farko Tattar ba su amince ba, amma da suka aiko wakilai suka gane ma idonsu gaskiyar lamarin yadda daular Musulmi tayi rauni sai suka amince. A bangaren halifa kuma sai waziri ya yi ta nuna masa cewa, ya kamata a yi sulhu da Tattar don ba a iyawa da su. A lokacin da suka iso kuma sai ya nemi iznin Halifa don ya tattauna da su a sansaninsu na bayan gari. Da ya je tare da mukarrabansa suka gama kitsa makircinsu sai ya dawo ya ce ma sarki an samu daidaitawa, kuma za a aurar da diyar sarkin Tattar ga dan sarki Musta’asim billah.
Suka kuwa gasgata shi, aka fita bayan gari da duk manyan gari masu mukaman sarauta da limamai da alkalai da malamai da dukkan masu alfarma su kimanin mutum 700. Haka suka tafi babu makami ko daya a tare da su. Sai da suka isa wurin tukuna suka gane wainar da waziri ke toyawa.
Da farko aka hana su isa sai 17 kawai daga cikin su. Daga bisani aka rika dibar su a hankali zuwa daurin auren da ba su gani ba. Aka rika tozarta su irin tozartawar da ba ta sifantuwa sannan daga bisani a kashe su a zo da wasu.
Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah ya kai mu Mu ciro muku wannan tarihi daga shafin Dakat Mansur Sakkwato.