Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta ayyana neman dan Majalisar Dokoki, mai wakiltar mazabar Bauchi, Yakubu Shehu Abdullahi ruwa a jallo, kan zargin hada kai wajen tada zaune-tsaye, hannu a kisan kai da kuma janyo rudani.
A wata sanarwa ta musamman da ‘yansanda suka fitar a ranar Litinin, na cewa, umarnin ya fito ne daga ofishin Sufeto Janar na ‘yansanda bisa zargin da ake wa Yakubu na hada kai wajen tada hankalin jama’a, haifar da rashin jituwa, yamutsa zaman lafiyan jama’a da kuma kisan kai.
- Ba Za Mu Amince Da Gazawar Kwamishinonin Zabe Bayan Daidaita Na’urar BVAS Ba – Shugaban INEC
- Gobara Ta Sake Tashi A Wani Kauye A Jihar Jigawa
Sanarwar ta roki jama’a da cewa duk wanda ya san inda za a ga Yakubu, ya taimaka ya sanar da ‘yansanda mafi kusa da shi ko kuma ya kira lambar wayo kai tsaye ta 08151849417.
Wakilinmu ya labarto cewa wannan umarnin bai rasa nasa ba da zarginsa da ake yi masa cewa na da hannu a rikicin baya-bayan da ya faru a garin Duguri, mahaifar gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad lokacin da tawagar dan takarar gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadik Baba Abubakar suka je yankin domin yakin neman zabe, lamarin da ya janyo mutuwar mutum guda da jikkata wasu da dama.
Kodayake batun ya juya ya zama cacar baki tsakanin APC da PDP inda kowa ke daura wa kowa laifin janyo rikicin.