A yammacin ranar Laraba da ta gabata ne, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisan jihohi wanda aka shirya za a yi a ranar 11 ga Maris zuwa ranar 18 ga Maris ta 2023.
A ranar 3 ga Maris ta 2023, kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta hana hukumar zabe kan goge sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisan tarayya da aka fara turawa ta na’urar BBAS, wanda ya gudana a ranar 25 ga Fabrairu sakamakon karar da dan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar kan kin amfani da na’urar wajen bayyana sakamakon zaben shugaban kasa.
- An Fitar Da Tsarin Yin Kwaskwarima Na JKS Da Hukumomin Gwamnati
- An Fitar Da Tsarin Yin Kwaskwarima Na JKS Da Hukumomin Gwamnati
Sa dai kuma hukumar INEC ta nuna adawa da wannan bukata, inda ta yi ikirarin cewa na’urar BBAS da masu shigar da kara suka nemi a dakatar da su za a yi amfani da su a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisan jihohi.
Hukumar INEC ta gabatar da cewa domin bayyana sakamakon zabe ta na’urar BBAS a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisan jihohi dole sai ta sake seta na’urorin, inda ta bukaci kotu kar ta amince da wannan bukata domin zai shafi zaben a ranar 11 ga Maris.
Dangane da hakan ne kotun daukaka kara da ke zaune a Abuja ta bai wa INEC izinin sake saita na’urar BBAS da aka yi amfani da su a wujen gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisan tarayya na ranar 25 ga Fabrairu.
Bayan yanke hukuncin ne hukumar INEC ta kira taro na sa’o’in da dama, inda ta yanke shawarar dage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisan jihohi da mako daya.
A wata sanarwa da Kakakin hukumar INEC, Festus Okoye ya fitar, ya bayyana cewa ba a dauki matakin da wasa ba, amma ya zama dole a tabbatar da cewa an samu isasshen lokacin da za a adana bayanan da aka ajiye a sama da na’urorin BBAS 176,000 daga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisan tarayya wanda ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun 2023, sannan a sake saita su a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.
A cewarsa, na’urar BBAS za a iya kunna ta ne kawai a kan takamaiman rana da lokacin da za a gudanar da zabe, inda ya ce kasancewar an yi amfani da su wajen gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga Fabrairun 2023, ya zama dole a sake saita fasalin na’urorin BBAS domin kunnawa a ranar da za a yi zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.
Bugu da kari, kakakin INEC ya kara da cewa, duk da cewa hukuncin kotu ya sa hukumar ta fara shirye-shiryen yin amfani da na’urar BBAS a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi, amma an makara kafin a kammala sake fasalin na’urar.
“Saboda haka, hukumar ta dauki matsaya mai matukar wahala, amma ya zama wajibi ta dage zaben gwamnonin da na ‘yan majalisun jihohi, wanda a yanzu za a gudanar da shi a ranar 18 ga Maris ta 2023. Sakamakon daukar wannan mataki, za a ci gaba da gudanar da yakin neman zabe har zuwa daren ranar Alhamis 16 ga Maris ta 2023, wato sa’o’i 24 kafin sabon ranar zaben,” in ji Okoye.
Kakakin INEC ya fayyace cewa wannan mataki bai saba wa masu kara da ke duba kayayyakin zabe ba. Ya yi alkawarin ci gaba da bai wa duk masu kara damar samun kayayyakin da suke bukata domin ci gaba da shari’arsu a kotu.
“Muna so mu tabbatar wa dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takara cewa za a adana bayanan da suke bukata daga zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya, an adana su a wuraren sirri da hukumar INEC ke ajiye muhimman kayayyaki da kuma hannun kwamishinonin zabe. Jam’iyyun siyasa za su iya neman asalin kwafin bayanan da ke cikin na’urar BBAS. Haka kuma sakamakon zabe da aka wallafa ta na’urar BBAS za su ci gaba da za a wurin kwamishinonin zabe domin jam’iyyu su samu damar samu a duk lokacin da suke bukata.”
Kafin dage zaben, INEC ta amince da cewa an samu kura-kurai tun daga kan na’urori da halayyar wasu jami’an zabe a matakai daban-daban, haka kuma dabi’un wasu wakilan jam’iyyu da magoya bayansu sun kawo cikas wajen gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya.
Tun bayan zaben na ranar 25 ga Fabrairu, hukumar zabe ta fuskanci suka daga masu sa ido kan zaben na cikin gida da na kasahen waje, ciki har da Chatham Hause da Amurka da Ingila da jam’iyyun siyasa da kuma masu sharhi kan harkokin siyasa da suka lura cewa amincewa da sakamakon zaben ya yi kasa, musamman ganin yadda INEC ta kasa bayyana sakamakon zaben ta na’urar BBAS tun a rumfunan zabe zuwa shafin INEC.
Sai dai kuma a wata ganawa da kwamishinonin zabe da ya gudana a shalkwatan hukumar INEC da ke Abuja, Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa abin da ke damun hukumar shi ne, yadda za a magance kalubalen da aka gano yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya kafin zaben gwamnoni 28 da kujerun majalisun jihohi guda 993.
Ya amince da cewa zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya sun tono matsaloli da dama da ke bukatar samun mafita cikin gaggawa, matsakaita da kuma na dogon lokaci.
A cewarsa, shirin zabe ya gudana cikin nasara, amma an samu kalubale wajen aiwatar da shi, wasu daga cikinsu ba a yi tsammani ba. Matsalolin kayan aiki da na’ura da halayyar wasu jami’an zabe a matakai daban-daban da dabi’un wasu wakilan jam’iyya da magoya bayansu sun kara dagula matsalolin da aka saba gani lokacin gudanar da zabe a Nijeriya.
Yakubu ya yi nuni da cewa, a yayin da hukumar ke kara fuskantar zabe a ranar Asabar, dole ne ta kara himma wajen shawo kan kalubalen da aka fuskanta a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, inda ya ce babu wani abu karbabbe ga ‘yan Nijeriya.
Ya ce dole ne a kammala rarraba kayayyakin aiki kwana daya kafin ranar zabe, inda za a mika su ga jami’an zabe da ke matakin kananan hukumomi. Ya yi nunu da cewa mayar da tsarin kamar yadda aka yi a wasu jihohi ya haifar da jinkiri wajen tura ma’aikata da kayayyakin zabe da kuma kawo tsaiko wajen fara gudanar da zaben a kan lokaci.
Yakubu ya yi gargadi cewa daga yanzu za a dora wa kwamishinonin alhakkin duk wani jinkiri ko rashin tura injin wutar lantarki zuwa cibiyoyin tattara sakamako ko rumfunonin zabe wurin da ake bukatar irin wadannan kayayyaki. Ya ce hukumar tana da isassun kayayyakin aiki a dukkan jihohin da ke kasar nan, kuma rashin tura su ba abin da ya dace ba ne.
Ya ce, “Sakamakon zaben ranar 25 ga Fabrairu, hukumar ta samu rahotanni daga ofisoshinmu na jihohi da korafe-korafe daga jam’iyyun siyasa da ‘yan takara. Inda aka tabbatar da kura-kurai wanda za a yi gyara. Dole ne in kara da cewa hukumar ba za ta tauye hakiin jam’iyyun da kuma na ‘yan takara wajen neman hakkinsu a kotu kamar yadda doka ta tanada.
“Duk ma’aikatan da aka samu da sakaci, ko asalin jam’in hukumar ko kuma ma’aikatan wucin-gadi ciki har da jami’an tattara sakamakon zabe, ba za su kasance cikin zabekan da ke tafe ba. Dole ne kwamishinonin zabe su fara aiwatar da daukan matakan ladabtarwa na gaggawa idan aka tabbatar da shaidar aikata ba daidai ba.”
Domin tabbatar da cewa duk wasu matsalolin da aka gano a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya bas u sake faruwa ba, shugaban INEC ya bayyana cewa dole ne a gudanar da horaswa da sabbin dubaru ga ma’aikatan wucin-gadi da suka shiga zaben da ya gabata. Ya kara da cewa a wuraren da aka sauya su da wasu saboda kwakkwaran dalilai, dole ne a horar da su yadda ya kamata saboda kar a samu jinkiri wajen gudanar da aiki.
Hakazalika, shugaban hukumar ya ce za a sake tura na’urar BBAS domin tantance masu kada kuri’a da kuma bayyana sakamakon zabe, inda ya jaddada cewa tura na’urar BBAS ya yi nisa wajen tantance masu kada kuri’a kamar yadda ake iya gani daga sakamakon zaben da ya gudana a kwanan nan.
Duk da kokarin da INEC ta ke yi na ganin komai ya tafi daidai da tsari a ranar Asabar, hukuncin da kotu ta yanke na iya kawo cikas ga shirin hukumar.
A ranar Alhamis da ta gabata ce, wata babbar kotun tarayya da ke zaune a Abuja ta umurci hukumar zabe da ta bai wa masu zabe katin zabe na wucin-gadi domin samun damar shiga zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a ranar 18 ga Maris.
Kotun ta bayar da wannan umarni ne biyo bayan karar da wasu mutane biyu da suka yi rajistan zabe, Kofoworola Olusegun da Wilson Allwell, inda suka koka da cewa duk da kokarin da suka yi na ziyartar ofishin hukumar INEC sun kasa samun katin zabe kafin cikar wa’adin amsa na ranar 6 ga Fabrairu.
Sai dai hukumar ta lashi takobin daukaka kara kan wannan hukuncin da kotu ta yanke na bai wa masu kada kuri’a katin zabe na wucin-gadi domin samun damar jefa kuri’a.
A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi ya fitar, ta tabbatar da cewa INEC za ta bi umurnin kotu, amma hukumar za ta dauki matakan da suka dace na kalubalantar wannan hukunci.
A cikin kalamansa ya ce, “An mika wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kwafin hukuncin da babbar kotun tarayya reshen Abuja ta yanke a yau, watta ta bayar da damar bai wa wasu masu kada kuri’a guda biyu katin zabe na wucin-gadi. Hukumar za ta dauki matakin gaggawa na daukaka kara kan wannan hukuncin kotun da ta yanke.”
Duk da tabbacin da hukumar INEC ta bayar game da shirye-shiryenta na zaben ranar Asabar, abin da ya faru a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya ya sanya akasarin ‘yan Nijeriya sun rasa kwarin gwiwa daga wurin hukumar. Domin haka, babban abin tambaya a nan shi ne, ko INEC za ta iya bai wa marada kunya a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi na ranar Asabar?
Dalilin Kasa Shigar Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Shafinmu Kan Lokaci
Hukumar INEC ta bayyana dalilin da ya sa aka samu matsala wajen shigar da sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a shafinta kan lokaci.
INEC ta kirkiri shafin na musamman (IReB) domin shigar da sakamakon zabe saboda inganta harkokin zabe a kasar nan.
Hukumar ta yi alkawarin shigar da sakamakon zabe tun daga runfunan zabe a cikin shafinta a kan lokaci.
Sai dai kuma shafin ya kasance ba ya aiki bayan an kammala kada kuri’a a wasu rumfunan zabe.
Da yake zantawa da gidan talabijin din Channels a wani shiri na harkokin siyasa a ranar Lahadin da ta gabata, Kakakin hukumar INEC, Festus Okoye ya bayyana abubuwan da suka faru lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu.
“Tabbas mun yi alkawarin cewa za a shigar da sakamakon zabe a kan lokaci a shafinmu, amma sai dai an samu kalubale masu yawa.
“Mun riga mun bayyana wa ‘yan Nijeriya cewa wadannan kura-kurai sun faruwa ne a daidai lokacin da ba mu yi tsammanin samun kalubale ba.
“Duk da kalubalen da muka fuskanta, mun yi kokari sosai wajen ganin an magance lamarin ta yadda idan muka zo lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi ba za mu fuskanci irin wadannan matsaloli ba,” in ji Okoye.
Abin Da Zai Faru Idan Aka Gaza Shigar Da Sakamakon Zaben Gwamnoni A Shafinmu
Huhumar INEC ta bayyana cewa ta gyara matsalolin da suka hana shigar da sakamakon zabe a shafinta gabanin gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a yi a ranar 18 ga Maris.
Kakakin INEC, Festus Okoye shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce a yanzu hukumarsa ta lalubo hanya ta biyu ko da an samu matsala wajen shigar da sakamakon zabe kai-tsaye a shafinta.
“Mun dauki matakai masu matukar muhimmanci, mun dauki darasi sosai daga zabukan da suka gabata, kuma mun lalubo hanya ta biyu ko da an samu matsala wajen shigar da sakamakon zabe kai-tsaye a shafinmu.
“Idan mun samu wani kalubale da ya shafi shigar da sakamakon zabe, ICT ta san abin da za mu yi domin ka da mu samu irin kalubalen da muka samu a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya,” in ji Okoye.
Ba Za Mu Lamunci Kuskure Daga Kwamishinonin Zabe Bayan Daidaita Na’urar BBAS Ba – Shugaban Hukumar
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bukaci kwamishinonin zabe da su tabbatar an gudanar da zabe cikin inganci da nagarta.
Yakubu wanda ya shaida hakan a lokacin ganawa da kwamishinonin zabe a Abuja, ya ce ba zai lamunci wani uzuri na kuskure ba, inda ya gargade su da cewa duk wata gazawa da aka samu a kowace jiha, to kuwa kwamishinan da ke kula da wannan jihar shi zai dauki alhakkin hakan, don haka kowa ya yi aiki tukuru domin tabbatar da ingancin zabe.
Babban Sakataren watsa labarai na shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi a hirarsa da LEADERSHIP a Abuja, ya bayyana cewa an yi ganawa da kwamishinonin zaben ne domin tattaunawa da muhawara ta karshe kan shirye-shiryen zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi tare da zabukan cike gurbi da za a gudanar ranar 18 ga watan Maris.
Ya ce kwamishinonin zabe sun tabbatar da cewa za su zage damtse su yi aiki tukuru domin gudanar da sahihin zabe mai ingataccen, sannan mai cike da adalci.
LEADERSHIP ta gano cewa an kira ganawar ne domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen kauce wa matsalolin da aka samu na dora sakamakon zaben kai-tsaye a shafin hukumar a lokacin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya wanda ya gudana a ranar 25 ga Fabrairu.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, zaben shugaban kasa na ‘yan majalisun jihohin sun taso da ayar tambaya game da yadda hukumar ta tantance masu kada kuri’a da na’urar BBAS, amma kuma ta gaza shigar da sakamakon zaben kai-tsaye a shafin hukumar, domin inganta sahihancin zaben.
Babu Abin Da Za Mu Boye – INEC
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa hukumar ba ta wani abu abin da za ta boye, kuma za ta samar da duk wasu kayayyakin zabe da muhimman takardun ga LP domin su duba wajen saukaka musu kan karar da suka shigar koitu na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar lauyoyi da kuma manyan jami’ai na LP suka ziyarci shalkwatan hukumar INEC domin neman samun muhimman takardun zabe da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga Fabrairu.
“Muna tabbatar wa tawagar louyoyi cewa hukumar INEC ba ta da wani abin boyewa, duk abin da kuke bukata, za mu ba ku,” in ji shi.
Yakubu ya kara da cewa an shirya wani taro da dukkan kwamishinonin zabe da ke jihohi 37 a fadin kasar nan, domin tattauna yadda za a samar da takardu da kayayyakin zabe ga LP da sauran jam’iyyu da suke bukaci hakan. Ya ce duk masu kara na neman hukumar ta ba kayayyakin za ta bayar tun daga matakin jiha har zuwa na tarayya.
“Rashin samar da takardun zai haifar da tunanin cewa da gangan INEC ta yi hakan, za mu tabbatar da cewa mun wanke kanmu daga wannan shari’a,” in ji shi.