Dai Bing, mukaddashin zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD ya yi kira ga kasashen da yake-yake suka addabe su, da su mai da hankali kan daidaita batun tsaro da na neman cigaba yadda ya kamata.
Dai Bing ya ce, galibin kasashen da suka taba fama da rikici suna fuskantar barazanar tsaro, kamar kungiyoyin masu dauke da makamai, da tsattsauran ra’ayi, da rikicin kabilanci, nuna karfin tuwo. Don haka, ya kamata hukumomin tsaro masu kwarewa su ba da tabbaci sosai wajen raya kasa.
Bugu da kari kuma, Dai ya ce, ko da yaushe kasar Sin na goyon bayan kasashen Afirka da su warware matsalolinsu bisa karfin kansu, kana tana goyon bayan kungiyoyin kasashen Afirka, da su taka muhimmiyar rawa tasu. Kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwa tare da sauran abokan huldar kasa da kasa, da karfafa goyon baya ga Afirka. (Kande Gao)