Game da kalaman da wasu kasashen yamma suka yi wai kasar Sin tana adana abinci daga kasuwar kasa da kasa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labarai cewa, kasar Sin tana da sharadi da karfi da kuma imani wajen samar da isasshen abinci ga al’ummun kasarta, kuma babu bukatar ta adana hatsi daga kasuwar kasa da kasa.
Wang Wenbin ya kara da cewa, tun bayan barkewar annobar cutar COVID-19, kasar Sin ta samar wa wasu kasashe tallafin abinci cikin gaggawa bisa shawarar MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa, don haka kasashen duniya sun yabawa kokarin da kasar Sin take domin samar da abinci ga al’ummun kasashen duniya, kana kasar Sin ita ma ta yi kira ga kasa da kasa cewa, bai kamata su barnata abinci ba.
A sa’i daya kuma Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, “Muna bakin cikin ganin yadda wasu kasashe masu tasowa suke fama da karancin abinci, amma wasu kasashe masu ci gaba suke zubar da abincin. Alkaluman da ma’aikatar aikin gona ta kasar Amurka ta fitar sun nuna cewa, a kowace shekara adadin abincin da Amurka ke batawa ya kai kaso 30 zuwa 40 bisa dari na daukacin abincin da ake samarwa al’ummun kasar, inda adadin ya kai tan miliyan 103 a shekarar 2018, wanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 161. Don haka, muna fatan wasu kasashen da abin ya shafa, za su rage abincin da suke batawa, haka kuma su sauke nauyin dake bisa wuyansu, ta yadda za a tabbatar da daidaiton cinikin kayayyakin aikin gona a kasuwar kasa da kasa, tare kuma da samar da isasshen abinci ga dukkanin al’ummomin kasa da kasa.” (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)