A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, sun gudanar da kebabbiyar ganawa a fadar Kremlin ta birnin Moscow fadar mulkin kasar Rasha.
Bugu da kari, a yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, ya gayyaci takwaransa na Rasha Vladimir Putin, da ya halarci taro na uku, wanda za a yi game da shawarar “ziri daya da hanya daya” domin hadin gwiwar kasa da kasa nan gaba cikin wannan shekara a kasar Sin.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da firaministan Rasha Mikhail Mishustin, ya ce ya gabatar da gayyatar ga shugaba Putin ne yayin wata ganawa da suka yi ba a hukumance ba.
Xi Jinping ya ce a baya ma shugaba Putin ya halarci taruka biyu da aka yi game da shawarar ta “ziri daya da hanya daya”, ya kuma bayyana shawarar a matsayin muhimmin jigo dake dunkule kasashen biyu.
Bugu da kari, shugaba Xi ya kuma yi kira da a ci gaba da tattaunawa tsakanin firaministocin sassan biyu, inda ya kuma gayyaci firaminista Mishustin da ya ziyarci kasar Sin. (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)