A bana ne ake cika shekaru 20, tun bayan da Amurka ta kaddamar da kai yaki a kasar Iraki. Wani nazarin jin ra’ayin jama’ar duniya da kafar CGTN ta gudanar, ya nuna cewa kaso 93.15 cikin 100 cikin mutanen da suka bayyana ra’ayinsu game da wannan yaki, sun nuna cewa, ya kamata Amurka ta dauki alhakin aiwatar da laifin yaki a Iraki.
A cikin shekaru 20 din da suka gabata, Amurka da kawayenta, sun kaiwa Iraki hari ba tare da samun izini daga MMD ba, bisa hujjar cewa, wani ta gano makaman kare-dangi a kasar Iraki. Amma daga baya, an tabbatar da cewa, Iraki ba ta da irin wadannan makamai. Wannan ya kara tabbatar da zalunci da nuna fin karfi na Amurka kan wasu kasashe.
Bayanai na nuna cewa, kaso 94.6 cikin 100 na yawan mutanen da aka ji ra’ayinsu na ganin cewa, babu wani dalilin da zai sa Amurka ta kaddamar da wannan yaki a Iraki, kuma yin hakan laifi ne.
A cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, yawan fararen hula da suka mutu, ko suka jikkata, ya kai fiye da dubu 200, yayin da wasu miliyoyin mutane suka rasa gidajensu. A nasu bangare kuwa, sojojin Amurka 4,572 sun mutu, kana yawan kudin da kasar ta kashe ya kai fiye da dala triliyan 2. Abin da duniya take bukata, shi ne zaman lafiya ba yaki ba.
A yayin da aka cika shekaru 20 da kaddamar da haramtaccen yakin Iraki, wajibi ne wasu ’yan siyasa na Amurka sun sake tunani don dakatar da ta da zaune tsaye a sauran wurare da sunan demokuradiyya, bai dace Amurka ta rika tilastawa kasashe bin tsarin demokiradiyarta ba. Ya kamata kasashe su zabi tsarin demokiradiya da ma na bunkasuwa da ya dace da yanayin kasashensu.
Masu sharhi na cewa, ko shakka babu harin da gwamnatin Amurka ta kaiwa Iraki da ma wasu kasashe a sassan duniya da sunan demokiradiya ko kare wani nau’i na muradunta, babban laifi ne. Kowane tsuntsun kukan gidansu yake yi.