Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi kira ga gwamnatin Amurka, da ta martaba salon gudanar da hada-hadar tattalin arziki bisa doka, da kiyaye ka’idojin takara mai tsafta, ta kuma dakatar da muzgunawa kamfanonin kasashen waje.
Tsokacin na Mao Ning, wadda ta yi yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa, ya biyo bayan bayyanar da shugaban kamfanin TikTok ya yi a gaban majalissar dokokin Amurka a jiya Alhamis.
Mao ta ce gwamnatin kasar Sin, bata taba umartar wani mutum, ko wasu kamfanoni su bayar da wasu bayanai, ko sirrika da suka shafi ayyukan su a kasashen waje ba, ta duk wata hanya da ta sabawa doka.
Ta ce “Har zuwa yanzu gwamnatin Amurka bata gabatar da wata hujja, dake tabbatar da cewa kamfanin TikTok na haifar da barazanar tsaro ga kasar ba, sai dai duk da hakan, ta rika furta wasu zarge-zarge bisa zato, tare da aiwatar da matakan muzgunawa kamfanonin da batun ya shafa. A hannu guda kuma, akwai wasu daga ‘yan majalissun dokokin Amurkan, dake bayyana matsin lambar da ake yiwa kamfanin TikTok, a matsayin muzgunawa mai nasaba da siyasa”. (Saminu Alhassan)