Tun bayan da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ratta hannu kan dokar bai wa matasa damar tsayawa takara, wannan lamari ya yi matukar zaburar da matasa wajen tashi tsaye domin shiga cikin harkokin siyasar kasar nan.
A baya dai, mafi yawancin matasa suna nuna halin ko-in-kula dangane da harkokin siyasan Nijeriya sakamakon wasu kalubale da suke fuskanta wanda ya hada da rashin kudade da kuma hana su damar shiga siyasa, amma a halin yanzu lamarin ya sauya zani.
- Zaben Gwamna: PDP Za Ta Yi Zanga-Zangar Kwana 7 Kan Sakamakon Zaben Nasarawa
- ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023
Siyasar 2023 ta zo da sabon salo, inda matasa da dama suka taka muhimmiyar rawa wajen kwato wasu kujeru daga cikin harkokin siyasar Nijeriya.
An dai samu dimbin matasa da suka samu nasarar lashe kujeru daban-daban a cikin harkokin siyasar Nijeriya a 2023. Wannan ya faru ne sakamakon tashi tsye da matasan suka yi wajen kwatan ‘yanci daga harkokin siyasar Nijeriya.
A karon farko a tarihin siyasan Nijeriya ba a taba samun lokacin da matasa suka zabura wajen shiga a dama da su a cikin harkokin siyasar kasar nan kamar wannan lokacin ba.
Alkaluma daga yawan masu rajistan zabe a 2023 na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ya nuna cewa matasa su suka fi yawa a wannan lokaci. Inda matasa masu shekaru 35 da suka kai adadin kashi 70 daga cikin rajistar zabe a 2023.
Hasalima dukkan ‘yan siyasan da suka tsaya takara a zaben 2023 sun dogara ne da samun goyon bayan matasa wajen samun nasarar cin zabe, domin su ne suke da yawan masu rajista da suka kai mutum miliyan 54 daga cikin miliyan 93 da suka yi rajistar zabe.
Matasa sun yi matukar samun kwarin giwa wajen tsayawa takara da kuma zaben wadanda suke so su shugabance su, sakamakon yawan da suke da shi a harkokin siyasar 2023.
Zaben 2023 ya kasance na musamman domin shi ne farkon zaben da aka gudanar karkashin wannan sabon dokar zabe. Ko shakka babu matasan Nijeriya sun yi matukar nuna sha’arsu na shiga harkokin zabe a 2023.
A cikin jam’iyyun siyasa 18 da suka shiga takara a 2023, babu jam’iyyar da ba a samu matasa da suka tsaya takara ba tun daga kujerun ‘yan majalisa na jiha da na tarayya da gwamnoni ciki har da na shugaban kasa.
Daga cikin matasan da suka samu nasarar a zaben 2023 sun hada da:
Rukayat Shittu ‘yar shekara 26 wacce ta samu nasarar lashe zaben ‘yan majalisa jiha na mazabar Owode/Onire a karamar hukumar Asa da ke Jihar Kwara.
Rukayat ta kasance fitacciyar ‘yar jarida ta tsaya takara ne a karkashin jam’iyya mai mulki ta APC.
Ta samu kuri’u 7,521 wadda ta doke abokin takararta na jam’iyyar PDP, Abdullah Magaji wanda ya samu kuri’u 6,957.
Zababbiyar ‘yan majalisar jihar ta nuna jin dadinta lokacin da aka bayyana ta a matsayin wadda ta samu nasarar lashe zabe da za ta wakilci mazabar Owode/Onire.
Ta bayyana godiyarta ga shugabannin jam’iyyar APC a jihar da kuma masu zabe da suka ba ta wannan dama na wakiltar al’ummar mazabar Owode/Onire.
“Ana mayar da matasa da mata saniyar ware a cikin harkokin siyasar Nijeriya, amma Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya sauya wannan dabi’a a Jihar Kwara. Zan tabbatar na inganta tare da karfafa gwiwar matasa da mata su shiga harkokin siyasa gadan-gadan,” in ji ta.
Zababbiyar ‘yar majalisar ta kasance shugaban sashin labarai na jaridar Just Ebent ta yanar gizo.
Hakazalika, matashi dan shekara 35 mai suna Lawan Musa ya samu nasarar kwace kujerar kakakin majalisar Jihar Yobe, Hon Ahmed Mirwa Lawan a karkashin jam’iyyar PDP na mazabar Nguru II.
Zaben dai ya yi zafi sosai, inda Musa ya samu nasara da yawan kuri’u da suka kai 6,648, yayin da Lawan ya samu kuri’u 6,466.
Jami’in da ke kula da zaben, Dakta Habib Muhammad ne ya bayyana sakamakon zaben, inda ya bayyana cewa sauran ‘yan takarar da suka tsaya a jam’iyyun ADC, NNPP da APM sun samu kuri’u 3,023 da 14.
Abin lura a nan shi ne, Hon Ahmed Mirwa Lawan ya kasance dan majalisa tun a shekarar 2003 lokacin da aka zabe shi a karkashin jam’iyyar ANPP.
Shi ma babban yaron gwamnan Jihar Kaduna Nasir el-Rufai, Bello el-Ruai ya samu nasarar doke dan majalisan tarayya mai ci a mazabar Kaduna ta Arewa.
Bello ya tsaya takara ne a karkashin jam’iyyar APC wanda ya samu nasarar doke Samaila Suleiman na jam’iyyar PDP, wanda ya kasance dan majalisa mai ci da ke wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa.
A cewar jami’in da ke kula da zaben, Farfesa Muhammed Magaji, Bello el-Rufai ya samu kuri’u 51,052, inda ya doke abokin takararsa na PDP wanda ya samu kuri’u 34,808.
Yayin da matashi mai shekaru 25, Muhammad Adamu Oyanki ya samu nasarar lashe kujerar dan majalisan jiha a mazabar Doma ta Arewa a karkashin jam’iyyar PDP.
Oyanki ya doke kakakin majalisan Jihar Nasarawa, Musa Ibrahim a zaben gwamnoni da na ‘yan jamalisar jihohi da aka kammala a makon da ya gabata.
A matsayinsa na dan shekara 25, zai kasance mafi kankantar shekaru a zauren majalisar Jihar Nasarawa.