Hukumar Tarayyar Turai ta amince da karin kudin tallafin samar da abinci na Yuro miliyan 600 ga Afirka da sauran sassan duniya wadanda ta ce ana bukatar su saboda rikicin Rasha da Ukraine.
Taimakon jin kan zai fito ne daga asusun raya kasashen Turai, a cewar shugaban hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen.
“Yakin Rasha da Ukraine yana cin zarafin mutanen Ukraine da Duniya baki daya.
“Rasha har yanzu ta hana fitar da miliyoyin ton na hatsi da ake bukata a duniya,” inji ta.
Tallafin ya hada da Yuro miliyan 350 don samar da abinci, Yuro miliyan 150 na taimakon jin kai, da kuma Yuro miliyan 100 da aka ware don Shirin Rage Talauci (PGRT) wanda Asusun Ba da Lamuni na Duniya ke gudanarwa (IMF).
Tallafin zai kai ga kasashen da abin ya shafa.
Kungiyar Tarayyar Turai ta ce tana sa ran shirin IMF zai hada kai da sauran masu ba da taimako na duniya don Taimakawa wadanda lamarin ya shafa.