Kafar CGTN ta kasar Sin ta gabatar da jerin bidiyo guda biyu a ranar 22 da 23 ga wannan wata, wato “tsarin demokuradiyya na jama’a” da kuma “demokuradiyya: daraja iri daya ta duk ‘yan Adam”, wadanda suka yi bayani game da cikakken tsarin demokuradiyya da ya shafi kowa da kowa na kasar Sin da kuma ma’anar demokuradiyya a matsayin daraja iri daya ta dukkan ‘yan Adam.
Wadannan jerin bidiyo biyu sun jaddada cewa, ba tsarin demokuradiyya daya ne kawai ke akwai a duniya ba, ya kamata a zabi tsarin demokuradiyya bisa yanayin kasa. Kuma burin tsarin demokuradiyya shi ne kara inganta zaman rayuwar jama’a, da baiwa jama’a hakkin samun girmamawa da daraja, kana tsarin demokuradiyya shi ne hakikanin tsarin demokuradiyya, wanda dukkan jama’a suke so. (Zainab)