Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci bikin bude taron bana na Asiya na Boao a lardin Hainan na kasar Sin, tare da gabatar da jawabi, bisa gayyatar da taron ya yi masa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ce ta sanar da hakan a yau Litinin.
A cewarta, firaministan Singapore Lee Hsien Loong, da takwaransa na Malaysia Datuk Seri Anwar Ibrahim da na Spaniya Pedro Sanchez da na Cote d’Ivoire Patrick Achi da manajan daraktar asusun ba da lamuni na duniya (IMF) Kristalina Georgieva, na daga cikin wadanda za su halarci taron bisa gayyatar da aka yi musu.
Har ila yau, bisa gayyatar da firaministan Sin Li Qiang ya yi musu, takwarorinsa na Singapore Lee Hsien Loong da na Malaysia Datuk Seri Anwar Ibrahim da na Spaniya Pedro Sanchez, za su yi ziyarar aiki a kasar Sin a gefen taron na Boao. (Fa’iza Mustapha)