Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Talata cewa, kasashe masu tasowa sun fi fuskantar hadarin basussuka a kwanakin baya sakamakon wasu batutuwan da suka shafi kasa da kasa, don haka wasu suke zargin kasar Sin kan tarkon basussuka, inda a cewarsu Sin tana bayar da rancen kudi ba cikin haske ba, zargin da kasar Sin ta musanta.
Mao Ning ta bayyana cewa, Sin tana bayar da goyon baya ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasashe masu tasowa. A cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen ginawa ko inganta hanyoyin jiragen kasa fiye da kilomita dubu 10, da hanyoyin mota kimanin kilomita dubu 100, da gadoji kusan dubu daya, da tasoshin jiragen ruwa kimanin dari daya, wadanda suka sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin wadannan kasashe da kyautata zaman rayuwar jama’arsu, da kawo musu hakikanin moriya.
Mao Ning ta kara da cewa, Sin ta gudanar da ayyuka bisa ka’idojin kasuwa da ka’idojin kasa da kasa, da girmama bukatun kasashen da abin ya shafa. Kuma kasar Sin ba ta tilastawa kowane bangare ya karbi rancen kudi ba, kana ba ta sanya sharudan siyasa a cikin yarjejeniyar bayar da basussuka ba. Ta ce zuwa yanzu, babu wani bangare da ya amince da zargin da aka yi wa kasar Sin kan tarkon basussuka. (Zainab)