Tsohon dan majalisar tarayya, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta 8, Sanata Shehu Sani, ya yi wa hukumar ‘yan sandan farin kaya ta Nijeriya DSS shagube kan ikirarinta na bankado wasu ‘yan siyasa marasa kishin kasa dake kokarin samar da gwamnatin wucin gadi a Nijeriya.
Shehu Sani ya kwatanta Hukumar DSS da irin tsarin Bokaye.
Shehu Sani ya ce, “Bokaye za su rika shaida wa mutanen da ke neman taimako ko kariya daga wurinsu cewa akwai masu kulla maka mugun tanadi amma ba za su bayyana sunayen wadanda suke kulla mugun tanadin ba ko kuma su baka wata alama da ke nuna ana aikata abinda suka yi zargi akai.”
Tsohon dan majalisar ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter.